Sai an bi diddigin duk wata dukiyar man fetur da ta bata shekaru 18 da suka gabata - Kotun Kolu ga Gwamnatin tarayya

Sai an bi diddigin duk wata dukiyar man fetur da ta bata shekaru 18 da suka gabata - Kotun Kolu ga Gwamnatin tarayya

Mun samu cewa a jiya Laraba kotun kolu ta Najeriya, ta gindaya wani umarni ga gwamnatin tarayya akan ta gaggauta fara shirye-shirye na bin diddiga da dawo da duk wata dukiya ta kudaden shiga na man fetur da ta bace shekaru 18 da suka gabata.

Kamar yadda shafin jaridar The Punch ya ruwaito, kotun ta umarci gwamnatin tarayya akan ta bibiyi duk wani diddigi na dawo da kudaden shiga da suka bace a sanadiyar hako man fetur da ma'adanan sa tun daga watan Agusta na 2003.

Wasu jiga-jigan lauyoyi bakwai na kasar nan bisa jagorancin Alkali Walter Onnoghen, sun rattaba hannu kan wannan umarni yayin da jihohin kasar nan uku da suka hadar da Rivers, Bayelsa da kuma Akwa Ibom suka shigar da korafin su akan gwamnatin tarayya tun shekaru biyu da suka gabata.

Jihohin uku sun shigar da wannan korafi da sanadin lauyan kolu na kowace jiha wajen neman hakkokin kasar nan, inda a ranar 6 ga watan Afrilun da ya gabata suka kulla wata muhimmiyar yarjejeniya ta gudanar da bincike tare da hadin gwiwar gwamnatin tarayya.

Sai an bi diddigin duk wata dukiyar man fetur da ta bata shekaru 18 da suka gabata - Kotun Kolu ga Gwamnatin tarayya
Sai an bi diddigin duk wata dukiyar man fetur da ta bata shekaru 18 da suka gabata - Kotun Kolu ga Gwamnatin tarayya
Asali: Facebook

Lauyan kolu na Najeriya, Abubakar Malami, shine wakilin gwamnatin tarayya da ya kulla wannan yarjejeniya da lauyoyin kolu na sauran jihohin uku da suka hadar da; Emmanuel Aguma na Rivers, Kemasuode Wogu na Bayelsa da kuma Uwemedimo Nwoko na Akwa Ibom.

KARANTA KUMA: Wutar Lantarki ta salwantar da Rayuwar wata Uwa da 'Ya'yanta 4 a jihar Neja

Jaridar LEGIT.ng ta fahimci cewa, manyan masana shari'ar za su hada kai tare da dukufa domin bin diddigi tare da dawowa da Najeriya arzikin ta da ya salwanta da alkalumma suka kimanta akan $1, 149, 750, 000, 000.

Lauyoyin cikin tarayya ra'ayi sun bayyana cewa, gwamnatin tarayya ta yi asarar wannan dukiya a sanadiyar rikon sakainar kashi na Ma'aikatar man fetur da ma'adanansa na fiye da shekaru 15 da suka gabata.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.legit.hausa&hl=en

Domin shawara ko bamu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://business.facebook.com/pg/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng