Yanzu Yanzu: An tabbatar da Bindo a matsayin dankarar gwamna na APC a Adamawa
Kwamitin Farfesa Oserheimen Osumbor sun yi watsi da korafe-korafe biyu da aka gabatar masu dake kalubalantar kaddamar da gwamnan a matsayin wanda yayi nasarar lashe zaben fidda gwani na gwamna a jihar wanda aka yi a ranar 5 ga watan Oktoba.
Mallam Nuhu Ribadu, tsohon shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa (EFCC) da Mahmood Halilu Ahmed wanda aka fi sani da Modi sunyi korafi akan kaddamar da Bindo a matsayin wanda ya lashe zaben fidda gwani.

Asali: Facebook
Sai dai daya daga cikin ýan takaran, Modi wanda ya kuma kasance kanin uwargidan shugaban kasa, Aisha Buhari ya yi watsi da hukuncin, cewa “Zan kalubalanci hakan a kotu”. Ya kuma kara fa cewa zai tabbatar da cewar kotu ta yi masa adalci.
Yayi zargin cewa mambobin kwamitin imma su kasance makusantan surikin Bindo ko kuma Adams Oshiomhole, shugaban APC na kasa.
KU KARANTA KUMA: Batan Janar: Rundunar soji ta gurfanar da mutane 13
A wani lamari na daban, mun ji cewa kungiyar Gwamnonin Najeriya (NGF) ta bayyana cewar ba ta adawa ta yiwa ma'aikata karin mafi karancin albashi da Kungiyar Kwadago na kasa ke nema.
Ciyaman din kungiyar, Gwamna Abdulaziz Yari na jihar Zamfara ne ya bayyana wa manema labarai hakan a jiya Laraba bayan kungiyar tayi taro a Abuja.
Ya ce matsalar ba wai adadin mafi karancin albashin da gwamnonin za su iya biya bane amma samuwar kudaden da gwamnonin za suyi amfani dashi domin biyan albashin da kungiyar kwadago (NLC) ke bukata.
Asali: Legit.ng