Shugaban Lauyoyin Najeriya ya sa an daure wani ja’irin ‘Dan Sanda

Shugaban Lauyoyin Najeriya ya sa an daure wani ja’irin ‘Dan Sanda

Shugaban Lauyoyin Najeriya Paul Usoro SAN ya bayyana cewa Jami’an tsaro sun kama wani ‘Dan Sanda da ya ci zarafin wani Lauya Abokin aikin su mai suna Luqman Bello a cikin Garin Ilorin kwanakin baya.

Shugaban Lauyoyin Najeriya ya sa an daure wani ja’irin ‘Dan Sanda
Shugaban 'Yan Sanda na Najeriya IG Ibrahim Idris
Asali: Depositphotos

A wani jawabi da Sakataren Shugaban Lauyoyin kasar ya fitar, ya tabbatar da cewa Jami’in ‘Dan Sandan da ya wulakanta wani Lauya Abokin aikin su yana hannun manyan sa inda aka casa sa a hannun Kwamishinan ‘Yan Sanda.

A jawabin na Kunle Edun a madadin babban Lauya Paul Usoro SAN, Lauyan ya bayyana cewa sun sanar da manyan ‘Yan Sanda yadda wani Jami’in su ya wulakanta wani Lauya da ke aiki a Ilorin har ya tube sa yayi masa mugun duka.

KU KARANTA: Kotu ta ba EFCC izinin rike Fayose na tsawon kwanaki 14

Dama can dai Shugaban NBA na Lauyoyin Najeriya ya nuna cewa ba za su amince da wannan wulakanci ba. Tuni dai har Sufetan ‘Yan Sanda ya shiga cikin batun inda aka garkame wannan ‘Dan Sanda a babban ofishin su da ke Kwara.

Shugaban Lauyoyi na Jihar Kwara Idowu Akande ya tuntubi ‘Yan Sandan Kasar lokacin da wannan abu ya faru inda shi ma Jami’an tsaron su ka kusa yi masa duka. Hakan ya sa babban Lauya Paul Usoro SAN ya dauki matakin kare Jami’in na sa.

Dazu kun ji labari an gano cewa Gwamna Nyesom Wike na Jihar Ribas ya ba hukumar zabe na kasa watau INEC takardan shedar haihuwa na bogi ne inda aka nemi a soma binciken Gwamnan na PDP.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng