Wata sabuwa: An fallasa wani gwamnan jam’iyyar PDP dake amfani da shaidar haihwua ta bogi
Wani abokin gwamnan jahar Ribas Gwamna Nyesom WIke, mai suna William Wobodo wanda yace tare da gwamnan suka yi karatu a tsangayar sharia na jami’a kimiyya ta jahar Ribas ya shigar da karar gwamnan gaban kotu akan yana amfani da takardar shaidar haiuwa ta bogi.
William wanda lauya ne mai zaman kansa ya shigar da karar gwamnan ne zarginsa da shirya shaidar haihuwa ta karya, kuma ya mikata ga hukumar zabe mai zaman kanta don samun samar shiga zaben gwamnan a shekarar 2019.
KU KARANTA: Ta’aziyya: Buhari ya kira mahaifin Hauwa Liman a waya don jajanta masa
Majiyar NAIJ.com ta ruwaito William ya bukaci babbar kotun tarayya dake jahar da ta haramta ma WIke shiga takarar gwamna na shekarar 2019 saboda ya shirya takardun haihuwa na bogi dake nuna shekarunsa 54 a yanzu, alhalin kuwa shekarunsa 50 a rayuwa.

Asali: Depositphotos
Lauyan ya shaida ma kotun cewa a shekarar 1999/2000 Wike ya nemi mukamin shugaban karamar hukumar Obia/Akpor, a lokacin bai wuce shekaru 35 ba, wanda shine karancin shekarun tsayawa takarar ciyaman a wannan lokaci.
Amma saboda bukata, sai Wike ya samu takardar rantsuwa dake nuna an haifeshi ne a shekarar 1963, 1 ga watan Maris, sai dai ita kanta takardar rantsuwar an ce an yi ta ne a shekarar 1986, amma karamar hukumar Obia/Akpor ba’a kirkireta ba sai a shekarar 1989, inji shi.
Haka zalika babu rattafa hannun kwamishinan rantsuwa na kotun da aka ce anyi takardar rantsuwar akai, don haka William ya bukaci kotu ta haramta ma WIke shiga zaben saboda mika ma INEC takardar shaidar haihuwa ta bogi.
Daga karshe William yace a lokacin da suke makaranta, WIke na amfani da shekarar 13/12/1967 ne, wanda yasa shi cika shekaru 50 a shekarar 2017, amma sai ya bayyana ma INEC cewa shekarunsa 54 a shekarar 2017.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar NAIJ.com Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.naij.com
Sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa za ta koma LEGIT.ng Hausa
Asali: Legit.ng