A shirye mu ke tsaf mu shiga Kotu da Ganduje – Mawallafin Daily Nigerian Jafar Jafar

A shirye mu ke tsaf mu shiga Kotu da Ganduje – Mawallafin Daily Nigerian Jafar Jafar

Mun samu labari cewa Mawallafin Jaridar nan ta Daily Nigerian wanda ta saki faifan bidiyon Gwamman Jihar Kano Dr. Abdullahi Ganduje yace a shirya su ke da a shiga Kotu a kan wannan batu da Mai Girma Gwamna.

A shirye mu ke tsaf mu shiga Kotu da Ganduje – Mawallafin Daily Nigerian Jafar Jafar
Ganduje ya ruga Kotu bayan an saki Bidiyon da ke zargin sa da aikin assha
Asali: Depositphotos

Jafar Jafar wanda shi ne Mawallafin Jaridar Daily Nigerian ya maida martani bayan jin labarin cewa Gwamnatin Jihar Kano ta sheka Kotu a sakamakon faifan da aka saki inda aka ga fuskar Gwamnan yana karbar Daloli.

Editan Jaridar wanda tayi wannan aiki ya bayyana cewa a shirya yake tsaf na shiga Kotu da Gwamnan na Kano. Jafar ya kara da cewa yana da wasu Bidiyoyin da zai fitar lokaci-bayan-lokaci domin tonawa Gwamnan na Kano asiri.

KU KARANTA: Bidiyon Gwamnan Kano yana cusa kudin rashawa a babbar riga

Gidan Jaridar dai ta shirya yakar wannan Gwamna da ake zargi da karbar cin hanci da rashawa. Jafar yace da gan-gan su ka cire muryar da ke cikin Bidiyon saboda wasu dalilai amma tuni wasu su ka ji abin da Gwamnan yake fada.

Gwamna Abdullahi Ganduje dai yace kokari ake yi a bata masa suna inda yace bidiyon bogi ne ya kuma kira jama’a su yi watsi da wannan abu yace kuma dole shari’a tayi aiki. Yanzu dai jama’a sun fara kiran a tsige Gwamnan na Kano.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa.

Mun gode da kasancewar ku tare da mu.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

Tags: