An kori ma'aikatan Radiyon Amurka 15 a kan karbar kyautar gwamnan APC

An kori ma'aikatan Radiyon Amurka 15 a kan karbar kyautar gwamnan APC

A lokacin da tawagar gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari, ta ziyarci ofishin yada labarai na gidan Radiyon Amurka, a ranar 9 ga watanwatan Janairu, 2018, babu wanda daga cikin ma'aikata 15 ya yi tsammanin cewar ziyarar gwamnan za ta jawo masu rabuwa da aikinsu.

Bayan gama ganawa da gwamna Masari a dakin watsa labarai, an zagaya da shi domin ganewa idonsa yadda aka kawata ginin ofishin.

A yayin da aka raka gwamna Masari domin yin bankwana da shi, sai daya daga cikin hadimansa ya bawa wani ma'aikacin sashen Hausa kunshin Dalar Amurka $5000.

Sai dai hadimin gwamnan, Abdu Labaran, ya musanta cewar gwamnan ba gwamna Masari ne ya bayar da kudin ba.

An kori ma'aikatan Radiyon Amurka 15 a kan karbar kyautar gwamnan APC
Ofishin Radiyon Amurka
Asali: Facebook

Daga baya ma'aikatan sashen Hausa na Radiyon Amurka sun raba kudin a tsakaninsu. Daga cikin ma'aikatan da su ka ci moriyar kyautar akwai Sahabu Imam Aliyu, Jummai Ali, Ladan Ayawa, Ibrahim Jarmai, Abdoulaziz Adili Toro, Ibrahim Alfa Ahmed da sauran su.

Shugaban sashen Hausa na Radiyon Amurka ne ya tona maganar bayan ya koma aiki daga hutun da ya yi a Najeriya.

DUBA WANNAN: Fitaccen tsohon dan wasan Najeriya ya sadaukar da gidansa don kamfen din Buhari

Dokar kasar Amurka ta haramtawa ma'aikatan Radiyon Amurka karbar kudi da ya kai dalar Amurka $20 yayin da su ke bakin aiki.

Tun a watan Oktoba ne gidan Radiyon ya fara bincike a kan batun tare da bawa ma'aikatan takardar dakatarwar daga aiki kafin daga bisani a sallame su bayan kammala bincike.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel