Yanzu-Yanzu: Wasu zababun 'yan majalisar wakilai na APC sun shiga bayan labule da Buhari

Yanzu-Yanzu: Wasu zababun 'yan majalisar wakilai na APC sun shiga bayan labule da Buhari

A halin yanzu shugaba Muhammadu Buhari ya na wata ganawar sirri da wasu zababun mambobin majalisar wakilai na jam'iyyar All Progresive Party (APC) a cikin dakin taro na Banquet da ke Fadar Aso Villa a Abuja.

Wannan taron na zuwa ne sa'o'i 24 bayan Jagoran masu rinjaye na majalisar dattawa, Ahmed Lawan ya shaidawa manema labarai cewar sanotocin APC sun dakatar da yunkurin tsige shugaban majalisa, Dr Bukola Saraki daga mukaminsa.

Yanzu-Yanzu: Wasu zababun 'yan majalisar wakilai na APC sun shiga bayan labule da Buhari

Yanzu-Yanzu: Wasu zababun 'yan majalisar wakilai na APC sun shiga bayan labule da Buhari
Source: UGC

DUBA WANNAN: Atiku ya zolaye Buhari a kan nadin ministoci

Mr Saraki da Kakakin majalisar wakilai na kasa, Yakubu Dogara sun sauya sheka daga jam'iyyar APC zuwa PDP ne bayan sun koka kan cewar an mayar da su saniyar ware a jam'iyyar.

Sai dai a halin yanzu, babu tabbas ko an kira taron ne domin tattauna matakin da za'a dauka a kan kakakin majalisar wakilai Yakubu Dogara.

Ku biyo mu domin karin bayani ...

Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel