An sake samun limamiya mace a Turai, jiya tayi bayanin matsayinta ga 'yan jarida

An sake samun limamiya mace a Turai, jiya tayi bayanin matsayinta ga 'yan jarida

- Limamiyar mata ta farko a kasar Denmark ta jagoranci masallacin mata sallah

- Mai neman hakkin musulmai ce da kuma hadin kan mata

- Khankan ta jagoranci masallacin Mariam dake Copenhagen, wanda dama mata ke jagorantar shi

An sake samun limamiya mace a Turai, jiya tayi bayanin matsayinta ga 'yan jarida
An sake samun limamiya mace a Turai, jiya tayi bayanin matsayinta ga 'yan jarida
Asali: Twitter

Limamiyar farko ta mata wacce ta jagoranci kungiyar masallacin mata dake Copenhagen mai suna masallacin Mariam. Mai kwato hakkin musulmai ce a abubuwan da suka danganci hadin kan mata. Tayi rubuce rubuce akan musulunci da siyasa a rayuwa.

Khankan haifaffiyar kasar Denmark cewa 1974, mahaifiyar ta yar kasar Finland, mahaifinta kuma Dan Syria.

Khankan tayi karatu a Damascus inda ta dawo Denmark a 2000. Tana da digiri na biyu a fannin zamantakewar addini da digirin digirgir daga jami'ar Copenhagen.

Masallacin da take jagoranci ya sha bambam da sauran masallatan Denmark saboda shi mata ke jagorantar shi. Akwai ire iren masallatan a US, Canada da Jamus.

DUBA WANNAN: Principal tayi wa gwamnati kwacen malamai

Khankan ta kirkiro kungiyar mai suna 'Critical Muslims' wacce ke da burin alakanta addini da siyasa.

An bude masallacin ne a watan Fabrairu Amma bai fara aiki ba sai watan Augusta. Khankan ke Kiran sallah inda mata 60 ke binta. Sabon masallacin ya daura aure masu yawa. Suna daura auren mutane masu bambancin addini, wanda wasu masallatan basa yi.

Sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa damu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel