Da duminsa: Bayan gano motar sa, sojoji sun kama wani mutum sanye da kakin janar Alkali, hoto
Bayan nasarar gano motarsa a wani tafin ruwa mai zurfin gaske dake unguwar Dura Du a karamar hukmar Jos ta Kudu, rundunar soji dake neman Manjo Janar Idris Alkali (mai ritaya) da ya bace tayi nasar cafke wani mutum sanye da kakin janar din.
A jiya ne Legit.ng ta kawo maku rahoton cewar hukumar sojin Najeriya ta gano motar Janar (mai ritaya) a karkashin wani kududdufi dake unguwar Dura Du a karamar hukumar Jos ta kudu, bayan fiye da sati uku ana nemansa.
Manjo Janar Idris Alkali ya bace ne tun ranar 3 ga watan Satumba a hanyarsa ta zuwa Bauchi daga Abuja. Rahotannin da hukumar soji ta tattara sun gano cewar Alkali ya bata ne a karamar hukumar Jos ta kudu.

Asali: Facebook
Babu tabbacin ko gawar Alkali na cikin motar. Sai dai Birgediya Janar Umar Mohammed, shugaban rundunar soji dake farautar neman inda Janar din yake, ya bayyana cewar zasu kwashe ruwan domin tabbatar da gawar Alkali na ciki ko akasin haka.
DUBA WANNAN: Hukumar sojin sama ta bude katafaren dakin binciken laifuka na kimiyya, hotuna
Tun a ranar 20 ga wata ne, Birgediya Janar Umar Mohammed, shugaban tawagar masu neman Janar Alkali, ya shaidawa gidan talabijin na Channels a yau, Alhamis, cewar sun tura rundunar soji zuwa yankin Dura Du dake karamar hukumar Jos ta kudu a jihar Filato.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng