Yajin aiki: Ku fitar da ran samun albashi a kan lokaci - Babban akawun tarayya ga ma'aikata

Yajin aiki: Ku fitar da ran samun albashi a kan lokaci - Babban akawun tarayya ga ma'aikata

- Bisa alamu ma'aikatan gwamnatin tarayya ba za su samu albashinsu na watan Augusta kan lokaci ba

- Wannan ya faru ne saboda yajin aikin Kungiyar Kwadago da jami'anta suka kulle ofishin Akanta Janar na tarayya, Mr Ahmed Idris

- Mr idris ya roki Kungiyar ta Kwadago da tsagaita yajin aikin domin shi da ma'aikatansa su samu damar shiga ofisoshinsu su biya albashi

Yajin aiki: Ku fitar da ran samun albashi a kan lokaci - Babban akawun tarayya ga ma'aikata
Yajin aiki: Ku fitar da ran samun albashi a kan lokaci - Babban akawun tarayya ga ma'aikata
Asali: Depositphotos

A yau, Alhamis ne Babban Akanta Janar na Tarayya, Ahmed Idris ya yi kira ga Hukumar Kwadago na kasa ta tsagaita yajin aikinta saboda ofishinsa ta samu damar kammala biyan albashin ma'aikata na wannan watan.

A jawabin da ya yi a Abuja, Mr idris ya ce fara yakin aikin ya janyo jami'an da ke aikin biyan albashi sun kasa samun damar shiga ofisoshinsu domin gudanar da ayyukansu na biyan albashin.

DUBA WANNAN: CBN ta kwace lasisin kamfanonin hada-hadar kudi 182 a Najeriya

Ya ya gargadin cewa biyan alabashi ba zai yiwu a irin wannan halin ba muddin ba'a kyale masu ruwa da tsaki sun shiga ofisoshinsu ba domin biyan albashin.

Ya ce yajin aikin zai sanya gwamnatin tarayya ta kasa biyan albashi ma'aikata kafin karshen wata kamar yadda ta yi alkawari a baya.

Mr Idris ya roki Kungiyar Kwadagon ta bawa ma'aikatansa damar shiga ofisoshinsu domin su biya ma'aikata albashin wannan watan. Ya ce shi da ma'aikatansa sun iso ofishinsu amma an hana su shiga.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel