Zaben Osun: PDP ta garzaya kotu

Zaben Osun: PDP ta garzaya kotu

Jam’iyyar PDP ta bayyana cewar zata tafi kotu domin neman a dakatar da hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) daga maimaita zabe a wasu mazabu a zaben gwamnan jihar Osun da aka kammala ranar Asabar tare da tilasta mata bayyana dan takararta a matsayin zakaran da ya lashe zaben.

A jawabin da sakatarenta na yada labarai, Kola Ologbondiyan, ya fitar a yau, Litinin, PDP ta ce an kamala zabe a dukkan mazabu da kananan hukumomin jihar Osun kuma an sanar da su, a saboda haka bata ga hujjar INEC na cewar za a je zagaye na biyu domin tabbatar da wanda ya yi nasara a zaben ba.

Dalilin INEC na cewar sai an koma zagayen raba gardama shine ba zata yiwu ta bayyana dan takarar PDP a matsayin wanda ya lashe zaben ba saboda adadin kuri'un da suka lalace a zaben sun fi adadin kuri'un da suka bashi rinjaye a zaben.

Sai dai jam’iyyar PDP ta fusata da wannan mataki da INEC ta dauka tare da bayyana cewar ana kokarin yi mata fashi ne da tsakar rana, kamar yadda yake a jawabin da sakatarenta na yada labarai, Kola Ologbondian ya fitar.

Zaben Osun: PDP ta garzaya kotu
PDP yayin yakin neman zaben Sanata Adeleke
Asali: Depositphotos

PDP ta kafe kan cewar dan takararta, Sanata Ademola Adeleke, ya lashe zaben bayan samun kuri’u mafi rinjaye a saboda haka ya zama wajibi hukumar INEC ta bayyana shi a matsayin wanda ya she zaben bisa dogaro da kwandin tsarin tsarin mulkin Najeriya da aka yiwa kwaskwarima a shekarar 1999.

Sashe na 179 (2) (a)(b) na kundin tsarin mulkin Najeriya ya fayyace, ba tare da wani rudani ba, waye ya zama zakara a duk zaben da aka gudanar,” a cewar jawabin na PDP.

DUBA WANNA: Zargin cin hancin makudan miliyoyi: ICPC ta gurfanar da Masari gaban kotu

Sannan ta cigaba da cewa, “kamar yadda yake a kundin tsarin mulki, mun cika sharuda biyu da suke tabbatar da nasara a zaben gwamna, wadanda su ne – (a) dan takara ya samu kuri’u mafi rinjayen kuri’un da aka kada sannan (b) kada jimillar dan takarar gwamna ya gaza samunkaso 1/3 na kuri’un da aka kada a kaso 2/3 na dukkan kananan hukumomin jihar daya yi takara.”

Bisa dogaro da wannan hujjoji, jam’iyyar PDP ta ce tana da yakinin kotu zata hana INEC gudanar da sabon zaben tare da tilasta mata bayyana dan takarar ta, Sanata Ademola Adeleke, a matsayin zakaran day a lashe zaben gwamnan jihar Osun.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel