Amfani 8 da gawayi zai iya yiwa lafiyar ku da muhallin ku

Amfani 8 da gawayi zai iya yiwa lafiyar ku da muhallin ku

Gawayi (bakin gawayi) na daga cikin abubuwan da aka fi wulakantar a gidajen mu. Jama'a da dama sun dauka amfanin gawayi ya tsaya ga girki ne kawai.

Sai dai gawayi na da amfani da yawa wajen inganta lafiyar jiki da tsaftace muhalli da mutane da yawa basu sani ba.

Amfani 10 da gawayi zai iya yiwa lafiyar ku da muhallin ku
Amfani 10 da gawayi zai iya yiwa lafiyar ku da muhallin ku
Asali: Twitter

1. Korar wari ko gyara gurbacewar iska

Shin takalmin ka sahu ciki na damunka da wari ko wani wuri a muhallin ku na yin wari? Saka gawayi cikin takalmi, firinji ko a daki zai yi maganin wannan matsala.

Gawayi na maganin warin jiki idan aka goga shi baya an kwaba.

DUBA WANNAN: Atiku ya bayyana sababbin rikicin makiyaya da manoma a Benue

2. Hana 'ya'yan itace da ganye lalacewa

Ga duk mai son kar kayan miya, ganye ko 'ya'yan itace su lalace sai ya saka su a cikin ruwan mai dauke da gawayi.

3. Hasken hakora

Ga duk mai son hakoransa su yi haske sai ya daka gawayi sannan ya sami icen agada yake dangwala yana goge hakorama ko kuma ya daka gawayi ya hada da gishiri yake wanke hakoransa.

4. Maganin tsamin miya

Shin kuna damuwa idan miyar ku ta lalace? Karshen damuwar ku ya zo. A mayar da duk miyar da tayi tsami kan wuta sai a dan saka gawayi daidai misali idan ta fara zafi. Gawayin zai cire dukkan tsamin da miyar tayi tare da dawo da dandanonta na asali.

5. Magance maye ko bugarwar giya

Amfani 8 da gawayi zai iya yiwa lafiyar ku da muhallin ku
Amfani 8 da gawayi zai iya yiwa lafiyar ku da muhallin ku
Asali: Twitter

Duk wanda ya sha giya bisa kuskure ko kuma yake tsoron ya sha giya da yawa, sai ya dan saka gawayi cikin kofin giyar ko kuma a wani sindarin lemo ya sha. Yin hakan zai warware duk wata illa da giya kan iya yi a jiki.

6. Taimakawa wajen warkewar ciwo

Babu bukatar a yanke wani sashe na jiki saboda ciwo ya rubar da shi. Duk ciwon da ya ki warkewa saboda kwayoyin cuta sun shiga ciki, sai ya samu garin gawayi yake zubawa a wurin. Hakan zai cire duk wata guba da kwayoyin cuta dake cikin ciwon. Ko yankewa mutum ya yi kuma yake son warkewa da wuri, kawai ya yi amfani da garin gawayi.

7. Tace ruwa/tsaftace ruwa

Zaku iya shan duk ruwan da ya gurbace idan ku ka zuba gawayi a ciki. Kada ku damu da kalar ruwan, koda kun ci gawayi ne ba zai yi maku illa ba.

8. Gyaran fata

Ga masu kuraje, kyasbi ko matsalar fata sai ya kwaba gawayi yake shafawa a jikinsa ko wurin da matsalar dake sannan ya barshi na wasu sa'o'i kafin ya yi wanka. Zai gyara maku fata, tayi laushi take sheki.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel