Jerin fitattun mata 5 da suka fi kowa kudi a Najeriya

Jerin fitattun mata 5 da suka fi kowa kudi a Najeriya

Tabbas duniya tana canzawa kuma zamani na shudewa wani sabo na zuwa da sabbin al'amurra da da baki ne musamman ma a kasar Najeriya da ma nahiyar Afrika baki daya.

A shekarun baya dai mata a wannan bangaren na duniya ba kasafai suke shiga a dama da su ba a harkokin kasuwanci, siyasa ko ma aikin gwamnati sabanin yanzu da kusan dukkan matakan da maza suka kai a da, yanzu ma mata na kokarin kai wa.

Jerin fitattun mata 5 da suka fi kowa kudi a Najeriya
Jerin fitattun mata 5 da suka fi kowa kudi a Najeriya

KU KARANTA: APC ta fitar da tsarin yadda zata tunkari zaben 2019

Wannan ne ma dai ya sanya yanzu ake bincike a kuma fiddo da jerin sunayen fitattun mata masu tarin dukiya kamar dai yadda ake yi wa maza suma.

Legit.ng dai ta tattaro maku jerin sunayen wasu mata 5 da suka fi tarin dukiya a Najeriya kamar yadda jaridar nan ta Forbes ta ruwaito:

1. Folorunso Alakija:

Ita dai wannan matar ita ce tafi kowace mace kudi a Najeriya. Tana harkokin kasuwanci a fannoni da dama ciki kuwa hadda harkar kwalisa watau 'Fashion design' da turanci da kuma harkar mai.

Yanzu haka itace shugaban kamfanin FARMA oil.

Tana da tarin duniyar da ta kai sama da dala biliyan 2 kuma tana da jirgin ta na kanta.

Yanzu haka tana da shekaru 67 a duniya.

Jerin fitattun mata 5 da suka fi kowa kudi a Najeriya
Jerin fitattun mata 5 da suka fi kowa kudi a Najeriya

2. Bola Shagaya:

Ita ma wannan hamshakiyar mai kudi ce da arzikin ta ya karade kasar nan dama nahiyar Afrika baki daya.

Hajiya Bola Shagaya dai musulma ce kuma ta taba rike shugaba ta mambobin amintattun bankin Unity na Najeriya.

Ita ma dai an kiyasta dukiyar ta da kusan Dalar Amurka biliyan 1 da miliyan dari tara.

3. Daisy Danjuma:

Ita dai wannan tana zaman matar daya daga cikin fitattun attajiran kasar nan watau Janar Theophilus Yakubu Danjuma kuma tana da kamfanoni da dama a ciki da wajen kasar nan.

Ita ma dai an kiyasta dukiyar ta da kusan Dalar Amurka biliyan 1 da miliyan dari bakwai.

4. Fifi Ejindu:

Duk da kasancewar ta matashiya, kyakkyawar budurwar tana da tarin dukiya mai yawa da ta samu ta hanyan wani kamfanin ta dake aikin gine-gine.

Matashiyar budurwar jika ce ga wani mashahurin sarkin daular Cobham dake a garin Kalaba mai suna Ekpo Bassey.

Ita ma dai an kiyasta dukiyar ta da kusan Dalar Amurka miliyan dari shida.

5. Dr Stella Okoli:

Wannan matar ma tana cikin fitattun attajiran mata a Najeriya da ta riga ta rika a harkar kasuwancin hada magungunan da miliyoyan 'yan Najeriya ke anfani da su.

Dakta Stella Okoli dai itace shugabar kamfaninin na hada magunguna na Emzor Ph8rmaceutical Industries Limited.

Ita ma dai an kiyasta dukiyar ta da kusan Dalar Amurka miliyan dari biyar.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel