‘Yan takaran PDP a zaben 2019 sun yi wani zama a cikin Garin Abuja

‘Yan takaran PDP a zaben 2019 sun yi wani zama a cikin Garin Abuja

Mun ji cewa masu neman takarar kujerar Shugaban kasa a karkashin Jam’iayyar adawa ta PDP sun hadu jiya Talata da yamma. Yanzu haka PDP na shiryawa zaben fitar da gwani da za ayi kwanan nan.

‘Yan takaran PDP a zaben 2019 sun yi wani zama a cikin Garin Abuja
Tsohon Gwamnan Jigawa Sule Lamido da Tambuwal wajen taron PDP
Asali: Depositphotos

Tsohon Mataimakin Shugaban kasa Atiku Abubakar, Ahmad Makarfi da kuma Shugaban Majalisa Bukola Saraki da tsohon Gwamnan Kano Rabiu Musa Kwankwasoda kuma Gwamnan Sokoto Aminu Tambuwal su na wajen taron.

Haka kuma sauran ‘Yan takara irin su tsohon Minista Kabiru Taminu Turaki da tohon Shugaban Majalisar Dattawa David Mark da tsohon Gwamnan Jigawa Sule Lamido da sauran masu neman Shugaban kasa irin su Datti Baba-Ahmed.

KU KARANTA: Atiku zai marawa duk wanda PDP ta tsaida baya wajen doke Buhari

Shugaban PDP na kasa watau Uche Secondus ne ya jagoranci wannan zama da aka yi. An samu halartar wasu Gwamnonin PDP irin su Gwamnan Bayelsa Seriake Dickson; da kuma Gwamnan Kwara Abdulfatah Ahmed da Ayo Fayose.

Kamar yadda mu ka samu labari daga Bukola Saraki an yi taron an tashi lafiya. Tsofaffin Gwamnoni irin su Alhaji Attahiru Bafarawa da Jonah Jang wadanda su na cikin masu neman kujerar Shugaban kasa sun halarci wannan zama.

Mun samu labari cewa wasu Magoya bayan Buhari sun kashe wani Direba har lahira bayan sun jefa sa lokacin da ya tuko Tawagar tsohon Mataimakin Shugaban kasa Atiku Abubakar zuwa Kaduna.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel