Dandalin Kannywood: Ali Nuhu ya bayyana fim din yafi so a rayuwarsa

Dandalin Kannywood: Ali Nuhu ya bayyana fim din yafi so a rayuwarsa

Shahararren tauraron harkar fina finan Hausa, Kannywood, Ali Nuhu da ake yi ma kirari da suna ‘Sarkin Kannywood’ ya bayyana fim din dayafi burgeshi tun daga farkon shigarsa harkar fim zuwa yanzu.

Gidan rediyon bbc hausa ta ruwaito Ali Nuhu yana bayyana cewa duk a cikin fina finan da yayi, bai taba yin fim din daya kai ‘Mansoor’ ba, sakamakon yayi amfani da kayan kimiyya da kuma kirkire kirkire da dama a cikinsa.

KU KARANTA: An bayyana abinda Buhari zai yi a yayin ziyarar da zai kai kasar China

A sanadiyyar Fim din Mansoor, Ali Nuhu ya lashe babbar kyauta a bikin karrama yan Fim da fina finan yankin Afirka da gidan talabijin na Afirka Magic ta shirya mai taken ‘Africa Magic Viewers Choice Award’ daya gudana a ranar Asabar a jahar Legas.

Dandalin Kannywood: Ali Nuhu ya bayyana fim din yafi so a rayuwarsa
Karramawar
Asali: Twitter

Bugu da kari Fim din Mansoor wanda aka yi shi akan labarin wani matashi da aka haifeshi na ta kan hanyar aure ba, kuma Ali Nuhu ya shirya kuma bada uamrni, ya lashe kyautar Fim mafi kayatarwa da aka shirya da harshen Hausa.

A cikin, Mahaifiyar Mansoor ta yi kokarin boye masa daya shafi asalinsa, amma fa daga bisani ya nemi sanin gaskiyar halin dayake ciki sakamakon soyayya data tunzura shi, bayan iyayen yarinyar dayake so sun yi masa gori.

A jawabinsa ga majiyar Legit.ng, Ali Nuhu yace wannan irin zarra da Mansoor yayi ya faranta masa, sa’annan yace Mansoor ya samu wannan nasara ce sakamakon anyi amfani da fasahar kirkire kirkire da na kimiyya a cikinsa, wanda ba’a taba samu a waninsa ba a Kannywood.

Ali Nuhu ya bayyana jigon shirin Mansoor a matsayin juriya da tawakkali a yayin da mutum ya tsunduma cikin mawuyacin hali, darasinda dake cikin shirin kuwa shine “Duk abinda aka ga ya samu mutum a rayuwa, kada ayi masa gori” Inji shi.

Daga karshe Ali Nuhu ya kara da cewa ya samu adadin kyautuka da lambobin yabo da dama tun daya fara hakar fim a basu taba kirguwa ba, duk da haka yace zai cigaba da shirya fina finai masu kayatarwa da ilimantarwa.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel