Magidanci ya sheme yayarsa har lahira kan zarginta da cinye masa diya da maita
- Ya kashe Yayarsa sakamakon yana zarginta da Maita
- Ayuba yace Yayartasa ce ta kashe masa diya
Rundunar Yansandan jihar Gombe ta yi ram da wani mutumi mai shekaru 39, Abubakar Ayuba kan zarginsa da kashe yayarsa sakamakon yana zarginta da mairta da tsafe tsafe, inji rahoton jaridar Daily Trust.
KU KARANTA: Mayakan rundunar Sojan kasa sun yi bore, sun kulle filin sauka da tashin jirage na Maiduguri
Majiyar Legit.ng ta ruwaito Ayuba, mazaunin unguwar Gangare dake garin Awak na cikin karamar hukumar Kaltungo yayi amfani da sanda ne wajen kashe Yayarsa mai shekarau 60 a rayuwa ne, Yabinu Ibrahim bayan ya zargeta da kama diyarsa ta hanyar maita har ta yi ajalinta.
Kaakakin rundunar Yansandan jihar, DSP Obed Mary Malum ta bayyana cewa sun kama Ayuba, kuma ana tuhumarsa da aikata laifin kisan kai, ta kara da cewa:
“Ayuba yayi amfani ne da sanda wajen dukan Yabinu babu kakkautawa har sai da ya ga ta mutu, sakamakon yana zarginta da kashe diyarsa mai shekara 25 Adama ta hanyar tsafi da maita, zamu gurfanar da shi gaban Kotu da zarar mun kammala bincike.” Inji ta.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng