Majalisar dattawa bazata samu zaman lafiya ba har sai tsoffin gwamnoni sun daina mayar da ita gidan ritaya – Donald Duke
Tsohon gwamnan jihar Cross River, Donald Duke ya bayyana cewa rikice-rikice a majalisar dokokin kasar musamman majalisar dattawa na faruwa ne saboda tsoffin gwamnoni sun mayar da ita gidan ritaya.
Dan takarar kujerar shugaban kasar ya wallafa a shafin twitter a ranar Laraba, 8 ga watan Agusta cewa majalisar dattawa ba zata taba samun zaman lafiya ba idan har aka cigaba da irin wannan al’ada.
Ya rubuta: “Majalisar dattawa ba zata samu zaman lafiya ba har sai tsoffin gwamnoni sun daina mayar da ita gidan ritaya.”
Legit.ng ta rahoto a baya cewa mukaddashin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo ya sallami shugaban hukumar yan sandan farin kaya, Lawal Daura.
KU KARANTA KUMA: An saki Lawal Daura, amma an kwace masa fasfo
Hakan ya biyo bayan mamayar da jami’an rundunar ta DSS suka kai majalisar dokokin kasar wanda ya haifar da tashin hankali.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng