Gwamnatin Tarayya za ta gyara titin Akwanga-Jos-Bauchi-Gombe
Yayin da Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya tafi hutun shekara a Birnin Landan na Kasar Birtaniya, Mataimakin sa Yemi Osinbajo wanda ke rike da kasar ya amince da wani namijin aiki da Gwamnatin Tarayya za tayi a Arewacin kasar.
A wajen taron Majalisar zartarwa na kasa na jiya, Mukaddashin Shugaban kasa Yemi Osinbajo ya amince da wani aikin titi da za ayi wanda zai tashi tun daga Garin Akwanga, ya shigo ta cikin Jos, ya kuma ratsa Bauchi har Garin Gombe.
Mun samu wannan labari ne bayan taron FEC da aka yi jiya a fadar Shugaban kasa wanda Mataimakin Shugaban kasa ya jagoranta da sauran Ministocin kasar. Wannan babban aiki da za ayi zai ci kudi har kusan Naira Biliyan 350 a shekaru 4.
KU KARANTA: 'Yan Kwankwasiyya sun bijirewa APC a Nasarawa
Ministan ayyuka da gidaje da na lantarki watau Babatunde Raji Fashola ne ya bayyana cewa Gwamnatin Tarayya ta amince da wannan aiki. Tsawon titin da za ayi ya haura kilomita 420. Za dai a gyara titin sannan kuma a fadada shi ta gefe.
Wannan hanya da ta ratsa Garuruwan Filato, Nasarawa, Bauchi da Gombe tana cikin hanyoyin da su ka hada Arewa maso Gabashin kasar da Arewa ta Tsakiya da Yankin Kudancin Kasar nan. A jiya ne aka yi taron FEC da aka saba kowane mako.
Kun san da cewa kwanan nan kuma za a gama titin dogon da zai hada Arewa da Kudancin Najeriya. Ministan sufuti yace Gwamnatin Buhari za ta gama aikin dogon jirgin kasan Warri kafin 2019.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng