Wani ya hallaka abokinsa don kawai yayi soyayya da budurwarsa
Wasu yan kungiyar asiri sun kashe wani matashi direban mota, Abraham Umar mai shekaru 28 a Cele bus stop, dake yankin Ijanikin na jihar Lagas.
Yan sanda sunce abokin wanda aka kashe ne ya shirya masa manakisa don kawai yayi soyayya da budurwar Abraham mai shekaru 17.
An tattaro cewa Abraham wadda aka fi sani da Abi, na cin abinci a gidan abincin mahaifiyar budurwars lokacin da yan bindiga suka kai hari wajen da misalin karfe 9 na daren ranar Talata.
An rahoto cewa sun harbi dan asalin jihar Benue din a kai, inda a take ya mutu.
Majiyarmu ta rahoto cewa an kai karar lamarin ga yan sandan Ijaniki sannan an kama budurwar mai suna Elo.
Idon shaida, wadda ya nemi a boye sunanshi yace yan bindigan sun zo ne a tawaga bayan Abraham ya ajiye motarsa yaje cin abinci.
Sai suka kai masa mamaya sannan suka harbe shi, inda a take kowa ya waste daga wurin.
Kanwar marigayin, Aminat Umar, yayinda take Magana cikin hawaye, tace wani abokin Abraham, Peter ne ya kai labarin ga yan uwan marigayin.
Mun samu labarin cewa margayin ya rasa mahaifinsa tun yana shekaru shida a duniya.
Marikinsa, Muhammad Umaru yace Abraham ya dade yana fuskantar sakonni na barazana daga wasu mutane da suka nemi ya daina soyayya da Elo.
KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Bamu daskarar da kowani asusun bankin Akwa Ibom ba - EFCC
Kawun marigayin ya bayyana shi a matsayin mutun mai sanyin hali kuma mara son tashin hankali.
Elo, wacce yan sanda suka kama tace Abraham ne saurayi daya da take da shi kuma bazata iya cewa ga dalilin kashe shi ba.
Kakakin yan sandan jihar Lagas, CSP Chike Oti yace an kama hudu daga cikin masu laifin.
Ya bayyana cewa aminin Abraham ne ya shirya masa manakisa saboda budurwarsa.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng