Za a cigaba da tsare tsohon Shugaban DSS har sai an kammala bincike a kan sa

Za a cigaba da tsare tsohon Shugaban DSS har sai an kammala bincike a kan sa

Mun samu labari cewa Gwamnatin Najeriya za ta cigaba da tsare tsohon Shugaban Hukumar tsaro na DSS Lawal Daura a cikin wani gida. Wata majiya daga Fadar Shugaban Kasa ta raya mana wannan.

Za a cigaba da tsare tsohon Shugaban DSS har sai an kammala bincike a kan sa
Tsohon Shugaban DSS yana shan tambayoyi a tsare

Jaridar Vanguard ta ji labari cewa za a cigaba da tsare tsohon Shugaban na DSS a wani katafaren gida inda yake amsa tambayoyi a tsare a halin yanzu. An gina wadannan gidaje ne a Fadar Shugaban kasar domin bada masaukin baki.

Yanzu dai Lawal Daura zai cigaba da zama a cikin Fadar Shugaban kasar na Aso Villa inda yake amsa laifuffukan da ake zargin sa da su. A farkon makon nan ne aka tsige Lawal Daura bayan ya aika Jami’an sa sun zagaye Majalisar Taraya.

KU KARANTA: EFCC za ta soma binciken wasu kudi da Lawal Daura ya lakume

Majiyar ta tabbatar da cewa ba za a saki Lawal Daura ba har sai an gama wasu bincike tukuna a kan sa. Daga cikin zargin da ke kan tsohon Shugaban na DSS, akwai wasu Dalolin kudi na Hukumar da ake tunani yayi awon gaba da su.

A Ranar Talata ne aka ji kwatsam Mukaddashin Shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo ya sallami Lawal Daura daga aiki. Bayan nan ne Jami’an tsaron da ke fadar Shugaban kasa su kayi wuf su ka tsare Daura su ka mika shi hannun Hukuma.

Kun ji labari cewa Mataimakin Shugaban kasa Yemi Osinbajo yayi magana da Shugaba Buhari wanda yanzu yake Landan inda ya fada masa cewa Lawal Daura yana aiki da Shugaban Majalisar Dattawa Bukola Saraki don haka ya kore sa.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng