Yanzu Yanzu: Osinbajo ya jagoranci zaman majalisar zartarwa
Mukaddashin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo ya jagoranci zaman majalisar zartarwa a yau Laraba, 8 ga watan Agusta.
Hakan ya kasance ne a daidai lokacin da shugaban kasa Muhammadu Buhari ke hutu a birnin Landan, inda ya mika ragamar mulki ga mataimakin nasa.
Karamin Ministan muhalli, Ibrahim Jibrin da karamin ministan man fetur, Ibe Kachikwu ne suka jagoranci bude taro da addu’a.
KU KARANTA KUMA: 2019: Bamu da wadda ya kai Buhari wajen sanyin hali – Kungiyar yakin zabe
A ranar Talata, 7 ga watan Agusta ne mukaddashin shugaban kasar ya sallami shugaban hukumar yan sandan farin kaya daga aiki.
Hakan ya biyo bayan mamayar da jami'an DSS suka kai majalisar dokokin kasar.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Ku leƙa shafukanmu na dandalin sada zumunta a:
https://facebook.com/naijcomhausa
https://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng