Wani Saurayi ya rasa gane kan Buduwarsa yayin da ta dinga zabga masa mari (Bidiyo)

Wani Saurayi ya rasa gane kan Buduwarsa yayin da ta dinga zabga masa mari (Bidiyo)

Soyayya gamon jini ce, amma fa idan ka kauna, haka zalika masu iya magan na cewa ita soyayya ruwan zuma ce, inda wani ya sha sai ya baiwa masoya suma su sha, anan kuwa akasin koyarwar soyayya aka samu a tsakanin wasu masoya biyu.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito wani dan Saurayi yayi kokarin jaddada soyayyarsa ga budurwar da yake tsananin kauna a tsawon rayuwarsa, tare da neman aurenta kamar yadda Turawa ke yi, a tsuguna a mika ma budurwa zobe.

KU KARANTA: Bahallatsar mamaye majalisa: Shugaban PDP ya roki Birtaniya ta dukunkuno Buhari zuwa Najeriya

Sai dai kash! Wannan matashi ya gamu da mummunan cikas, inda a yayin da yayi kokarin jadda soyayyar tasa ga budurwa, sai reshe ya juye mujiya, kalli kuma ya koma sama, inda ta zazzabga masa mari ba kakkautawa.

Ganin yadda budurwar nan ke sharara ma saurayinta mari, sai jama’a suka yi kawanya suka zagayesu suna kallon ikon Allah, suna mamakin yadda farar daya masoya sun sauya zuwa makyiya.

Sai dai gogan naku bai hakura ba, inda ya fara neman jama’a da zasu shiga tsakani don baiwa budurwarsa hakuri, amma ina, duk wanda ya janyo sai ya janye jikinsa, daga karshe dai ya cigaba da bin budurwar yana bata hakuri, ita kuwa marinsa kawai take yi.

Kai Jama'a, wannan wani irin soyayya ne, ko dai son masu wani ne, koshin wahala?

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel