Rai bakon Duniya: Ba duka ba zagi wani mutumi ya fadi matacce a tashar Mota

Rai bakon Duniya: Ba duka ba zagi wani mutumi ya fadi matacce a tashar Mota

Mutuwa rigace ba ta fita, kamar yadda wani mawaki yaka fadi, kuma dama idan ajali yayi kira, ai ko ba cuta sai an je, wannan shine kwatankwacin lamarin da ya faru a jihar Legas, inda wani mutumi ya fadi matacce babu sididi babu sadada.

Legit.ng ta ruwaito wannan mutuwar fuju’a ta faru ne a tashar Mota dake Orile Iganmu a ranar Talata, 7 ga watan Agusta, inda rahotanni suka bayyana cewa mutumin ya tafiya ne kawai ya fadi, ko da aka duba tuni ya rigami gidan gaskiya.

KU KARANTA: Mamaye majalisa: Sanatan Jam’iyyar PDP ya wanke Lawal Daura da soso da sabulu

Wani mai shago dake kusa da inda lamarin ya faru, Yinus Olayiwola ya bayyana cewa yana shagonsa da misalin karfe 6:30 na safe ya hangi mutumin yana ta rawar sanyi sakamakon ruwan sama dake dukansa.

Rai bakon Duniya: Ba duka ba zagi wani mutumi ya fadi matacce a tashar Mota
Mamacin

Shima wani mazaunin yankin da lamarin ya faru a idonsa, Bamidele Adejoke ya musanta jita jitan cewa mutumin mahaukaci ne, inda yace da hankalinsa, kawai dai rashin lafiya ne ya addabe shi, don haka yayi kira ga jama’a da su dinga kulawa da lafiyarsu.

Sai dai Bamidele ya bayyana bacin ransa da yadda har bayan awanni takwas hukumomi basu dauke gawar mamacin ba, inda yace hakan cin mutuncin mamacin ne.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Tags: