Zan warewa harkar ilmi kashi 21% cikin kasafin kudin Najeriya idan na zama Shugaban kasa inji Atiku
- Atiku Abubakar zai fito takara a zabe mai zuwa a karkashin PDP
- ‘Dan siyasar ya bayyana yadda zai gyara ilmi idan ya hau mulki
- Najeriya dai tana cikin ci-ma-baya a wajen harkar ilmi a Duniya
Tsohon Mataimakin Shugaban kasar nan Atiku Abubakar wanda ya ke kuma neman takara a 2019 yayi wa ‘Yan Najeriya babban alkawari game da harkar ilmin da ya tabarbare idan aka zabe sa a PDP.
Atiku Abubakar wanda yake sa ran karbe mulki daga hannun Shugaba Buhari yace idan har yayi nasara a 2019, zai warewa harkar ilmi kashi 21% na kasafin kudin kasar. Hakan dai har ya haura tsarin Majalisar Dinkin Duniya watau UN.
KU KARANTA: Da in bar PDP gara in bar siyasa a Kasar nan - Makarfi
Wazirin na Adamawa yace akwai abin koyi kwarai daga tunbatsar da Kamfanin Apple yayi a Duniya. Majalisar Dinkin Duniya tana kokarin ganin Kasashen Afrika sun inganta harkar ilmi wanda yake koma baya kwarai a kasashen.
Atiku wanda yake neman mulkin Kasar a PDP ya nemi jama’a su zabe sa domin gyara matakin ilmi. Har yanzu dai Gwamnatin Najeriya ba ta kashe abin da ya kamata wajen habaka ilmi da kuma kiwon lafiyar jama’a a Kasar nan.
Atiku Abubakar ya bayyana wannan ne ta bakin ofishin yakin neman zaben sa. Atiku yayi wannan jawabi ne bayan Kamfanin nan na Apple na Amurka ya ba Dala Tiriliyan 1 baya inda yace sanin darajar ilmi ya kai ga haka.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng