Google station: Za a bude wuraren hawa yanar gizo 200 a cikin Najeriya

Google station: Za a bude wuraren hawa yanar gizo 200 a cikin Najeriya

Kwanakin baya Mataimakin Shugaban Kasar Najeriya Farfesa Yemi Osinbajo ya kai ziyara zuwa Silicon Valley inda ya gana da manyan Jami’an kamfanin Google da kuma Kamfanin LinkedIn.

Google station: Za a bude wuraren hawa yanar gizo 200 a cikin Najeriya

Google ta shirya bude tashoshin hawa yanar gizo

Kamfanin Google da ke Turai ta shirya bude tashoshin da Jama’a za su hau yanar gizo na manhajar Wi-Fi. Google din za ta ba mutanen Najeriya damar amfani da yanar gizo ba tare da sun kashe ko sisin kobo ba a Duniya.

Google za ta kafa tashoshin na hawa yanar gizo da na’urorin zamani a manyan Garuruwa. Yanzu haka dai akwai wannan tasha ta Google a filin jirgin sama na Murtala Muhammed da ke Garin Ikeja a cikin Jihar Legas.

KU KARANTA: Wani Sarkin gargajiya yace ya fi Dangote kudi a Duniya

Google din za ta kawo tsarin “free WiFi for all” a wurare akalla 200 a manyan Garuruwa 5 na Najeriya. Ana sa rai za a kammala wannan aiki kafin shekarar 2019. Za a fara wannan tsari ne dai yanzu da cikin Garin Legas.

Kafin nan Kamfanin Google ta bude irin wannan tashoshi a Kasar Indiya, Thailand, Mexico, da kuma Kasar Indonesiya. Yanzu a shekarar nan an sa Najeriya cikin jerin Kasashen da za su amfana da wannan tsari a Duniya.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel