Na gwammace na bar siyasa dana bar jam'iyyar PDP - Makarfi

Na gwammace na bar siyasa dana bar jam'iyyar PDP - Makarfi

- Makarfi yace daya canja jam'iya gwara yabar siyasa gaba daya

- Zamu iya barin Saraki akan kujerar sa saboda bai sabawa kundun tsarin mulki ba

Na gwammace na bar siyasa dana bar jam'iyyar PDP - Makarfi
Na gwammace na bar siyasa dana bar jam'iyyar PDP - Makarfi

Alhaji Ahmed Makarfi ya bayyana yiyuwar barin sa jam'iyar PDP idan bai samu damar samun tikitin zaben 2019.

Yace zai bar siyasa baki daya maimakon ya koma wata jam'iyar.

Makarfi ya bayyana haka ne a ranar Asabar yayin da yake ganawa da manema labarai a sakateriyar PDP dake Minna dake Jahar Niger

DUBA WANNAN: Hukumar EFCC ta sako wasu ma'aikatan hukumar JAMB a gaba

Kamfanin dillancin labarai ya bayyana cewa Makarfi ya halarci Minna ne don neman goyan bayansu akan kujerar Shugaban kasa a 2019

Yace "Idan zanbar PDP to zanbar siyasa baki daya. Da ace zanbar PDP da tuntuni na bari to har yanzu babu damar barin".

"Wasu mutanen da an zungure su(ya taba kafadar sa) sai su koma wata jam'iyar a lokacin sai na dakata, ku kuma saiku karbesu a gidanku sannan ku basu dakin baki, daga baya saisu koma dakuna abu na karshe kuma sai su kore ku daga gidan naku, to mu bazamu kyale hakan ba kuma bazamu basu wannan damar ba saboda haka bazamu rarraba mutanen mu ba".

Makarfi yace zamubar Bakola Saraki akan kujerar sa ne saboda bai sabawa kundun tsarin mulki ba saboda barinshi APC zuwa PDP.

Makarfi dai tsohon gwamnan jahar Kaduna ne sannan yana rike da mukamin Ciyaman na PDP na kasa.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel