Ba sauki: ‘Dan jaridar da DSS su ka rufe tun a 2016 yace yana cikin wani hali
Wani ‘Dan jarida mai suna Jones Abiri da ya fi shekara 2 yana daure a hannun Jami’an DSS yayi magana inda ya koka da irin wahalar da yake fama da ita yana mai addu’a Allah ya kawo masa sauki.
Jami’an DSS ne su ka garkame Jones Abiri inda ake zargin sa da ta’addanci a Yankin Neja-Delta. A 2016 Jami’an tsaro su ka kama ‘Dan Jaridar a Garin Yenogoa da ke cikin Jihar Bayelsa sai dai ba a soma shari’a ba sai kwanan nan.
Ana zargin ‘Dan jaridar da neman makudan kudi daga Kamfanin man Agip da kuma Shell. Shi dai ‘Dan Jaridar ya bayyana cewa bai san da wannan laifi da ake zargin sa da shi ba. Tun a watan Yulin 2016 aka kama Abiri aka garkame.
KU KARANTA: Ba zan cuce ku ba, ba kuma zan yarda wani ya cuce ku ba In ji Buhari
‘Dan jaridar yana aiki ne da wani kamfani mai suna Weekly Source Newspaper da ke aiki a Yankin Neja Delta. Wannan Bawan Allah yace yana nan rai hannun Allah game da wannan mawuyacin hali da ya tsinci kan sa a hannun Jami’an tsaro.
Jones Abiri ya bayyana cewa Jami’an tsaron sun rike sa cikin mutunci amma ya nuna cewa yana shan wahala kwarai da gaske. Ana zargin sa da hada-kai da Tsagerun Neja-Delta wajen karbar kudi daga wasu manyan Kamfunan mai a Yankin.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng