'Yan Najeriya sun daina siyasar jam'iyya yanzu, cancanta suke bi - Garba Shehu
- Shugaba Buhari zai tafi hutun kwanaki 10
- Garba Shehu ya ce yanzu 'yan Najeriya cancanta suke bi ba jam'iyya ba
- Jam'iyyar PDP na zargin anyi haka ne don a gabatar da wata manuma a cikin gwamnatin Buharin
A zargin da babbar jam'iyyar adawa take yi ta Peoples Democratic Party PDP na cewar shugaban kasa Muhammadu Buhari ya dauki hutun kwana goma ne domin ya baiwa wasu na cikin gwamnatin sa damar yin abubuwan da basu kamata ba, wannan zargi bai kamata ba.
Tsarin da shugaban kasar ya dauka abu ne mai kyau, domin zai baiwa mataimakin sa damar gabatar da mulki na kwana 10, wanda jam'iyyar PDP ta kasa yi duk da tsawon shekarun data dauka tana mulkin mallaka.
DUBA WANNAN: Takardar bogi: SERAP ta baiwa hukumar NYSC kwanaki 7 ta gabatar da shaida akan Kemi Adeosun
Domin kawar da zargi, ku sani cewa Mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo SAN, wanda zai karbi rikon kwarya idan shugaban kasa bayanan, babban lauya ne wanda ya karbi kyaututtuka daban daban a gida da kasashen waje. Saboda haka gwamnatin APC ba ta yi kama da gwamnatin da zata dauki wata hanya da jam'iyyar PDP ta bi ba.
Muna maraba da duk wasu maganganun ku na kushe da kuke yi, amma ku sani yanzu 'yan Najeriya ba siyasar jam'iyya suke yi ba, suna bin cancanta ne, saboda haka sun gane duk wani kokari da kuke yi na yiwa shugaban kasa zagon kasa akan irin ayyukan da yake yi a kasar nan.
Shugaba Muhammadu Buhari ya dauko ayyuka masu muhimmanci da wahala a kasar nan, irin su kawo hanyoyi na saukaka kasuwanci, fito da asusun bai daya wato Treasury Single Account, TSA, kawo shirin tona barayin gwamnati, da daruruwan tsare masu muhimmanci, wadanda suka hada da dawo da sufurin jirgin kasa, gyara wutar lantarki da hanyoyi. Inda ace PDP ta yi wadannan ayyukan a shekaru 16 da tayi tana mulki da yanzu Najeriya ta kai wani babban matsayi a duniya.
Ko ina kasar nan an dage da yaki da cin hanci da rashawa, kuma kowanne dan Najeriya yana murna da hakan, yanayin tattalin arziki ya canja sosai, hakan wata shaida ce da ke nuna cewa wannan gwamnatin tana bin tsarin dimokradiyya sannan kuma tsarin tafiyar da tattalin arzikin ta ya gyaru, amma su 'yan jam'iyyar PDP hakan baya yi musu dadi, saboda idon su ya rufe wurin neman mulki.
A karshe wani abu guda daya da ya kamata 'yan Najeriya su sani shine, har yanz yakin bai kare ba, domin kuwa duk lokacin da jam'iyyar PDP ta kara dawowa mulki to fa komai zai dawo sabo ne, kasuwar cin hanci da rashawa zata sake budewa.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng