Sauya shekar Tambuwal: Idan na koma Sokoto za ku san wanene mai gida – Wamakko
Aliyu Wamakko, sanata mai wakiltan Sokoto ta arewa, yace nan da yan kwanaki masu zuwa za’a san wadda ke da ikon jan ragamar jihar.
Wamakko ya bayyana hakan a martanin san a sauya shekar Aminu Tambuwal, gwamnan jihar, inda ya bar jam’iyyar Progressives Congress (APC) zuwa jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP).
Tambuwal ya kasance kakakin majalisar wakilai da aka zaba karkashin lemar PDP amma ya sauya sheka zuwa APC a 2014.
Ya lashe tikitin zama takarar gwamna a lemar APC sannan ya yi nasarar kayar da dantakarar PDP a 2015.
KU KARANTA KUMA: Ndume, Adamu, Omo-Agege na kulla makirci don tsige Saraki – Yan majalisa na PDP
Wamakko yayi sharhi akan sauya shekar Tambuwal lokacin wata hira a laabaran NTA, cewa Sokoto na APC ne.
Yace mutanen jihar na bayansa da sauran majalisa dake APC har yanzu.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng