2019: Shugaba Buhari ya aikawa Mama Taraba wata wasika mai muhimmanci
- Shugaba Buhari ya nuna goyon bayan sa dari bisa dari ga tsohuwar 'yar takarar gwamnan jihar Taraba, Aisha Alhassan wacce aka fi sani da Mama Taraba
- Yayi alkawarin tabbatar da zabe cikin aminci da kwanciyar hankali a fadin kasar nan
A wata wasika da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya aikawa da tsohuwar 'yar takarar gwamnan jihar Taraba kuma ministar harkokin mata a yanzu, Hajiya Aisha Jummai Alhassan, shugaban kasar ya nuna goyon bayan shi dari bisa dari akan kokarin da take na sake fitowa takarar gwamnan jihar Taraba a karo na biyu.
DUBA WANNAN: 'Yan majalisar Tambuwal 12 sunki binshi PDP, sun nuna goyon bayan su ga shugaba Buhari
Ga abinda shugaban kasar ya ce a wasikar tashi.
"Na samu wasikar ki a yau da take nuna mini burin ki na sake fitowa takarar gwamnan jihar Taraba a karo na biyu.
Bari nayi miki godiya a madadin dukkanin al'ummar Najeriya da irin kokarin da kika yi wurin bada lokacin ki wurin kawo cigaba ga wannan gwamnati. Na san irin kokarin da kika yiwa jam'iyyar APC a zaben da ya gabata na shekarar 2015.
Kamar yanda kika sani, a halin yanzu hankalina ya koma kan tabbatar da cewar an yi zabe mai aminci a kasar nan. Sannan burin mu shine mu goyawa duk wani dan jam'iyyar APC baya domin ya samu nasara. Saboda haka ina yi miki fatan alkhairi a kokarin da kike na zama gwamnar jihar ki. Sannan ina tabbatar miki da cewar duk wata hukumar tsaro da ma'aikatu dama hukumar zabe ta kasa zasu samu goyon bayana dari bisa dari wurin gabatar da zabe cikin zaman lafiya da kwanciyar hankali a shekarar 2019."
A shekarar 2015 dai Hajiya Aisha Alhassan ta taba fitowa takarar gwamnan jihar Taraba bata samu damar hayewa ba, to a wannan karon ma dai ta fito da niyyar tsayawa takarae gwamnan jihar.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng