Abubuwa 8 da baku sani ba game da tafiyar shugaba Buhari kasar Togo

Abubuwa 8 da baku sani ba game da tafiyar shugaba Buhari kasar Togo

A ranar Lahadin da ta gabata ne shugaban kasa Muhammadu Buhari tare da tawagar sa suka shilla birnin Lome na kasar Togo domin halartar muhimman taruka biyu da suka shafi kungiyar kasashen Afirka ta Yamma.

Kamar yadda kafofin watsa labarai na kasar suka bayyana, hadimin shugaba Buhari kan harkokin hulda da manema labarai, Mallam Garba Shehu, shine ya bayar da wannan sanarwa a ranar Asabar din da ta gabata.

Abubuwa 7 da baku sani ba game da tafiyar shugaba Buhari kasar Togo
Abubuwa 7 da baku sani ba game da tafiyar shugaba Buhari kasar Togo

Binciken shafin jaridar Legit.ng ya kawo muku jerin wasu ababe da baku da masaniya a kai da suka shafi tafiyar shugaba Buhari kasar Togo:

1. Domin tattauna al'amurran barazanar tsaro musamman ta'addanci da suka shafi kungiyar kasashen yankin Afirka ta Yamma.

2. Tattauna al'amurran tattalin arziki da suka shafi mayar da kudin bai daya a kungiyar kasashen Afirka ta Yamma.

3. Gudanar da taro na 53 na shugabannin kungiyar kasashen Afirka ta Yamma inda za a tattauna al'amurran siyasa da tsaro da suka shafi kasashen Guinea Bissau, Mali da kuma Togo.

4. Tawagar gwamnoni da suka ziyarci kasar Togo tare da shugaba Buhari sun hadar da; gwamna Ben Ayade na jihar Cross River da kuma Gwamna Abubakar Bello na jihar Neja.

KARANTA KUMA: Hukumar 'yan sanda ta daƙume wani 'Dan Acaɓa bisa laifin yiwa wata Yarinya 'yar shekara 11 Fyaɗe a jihar Neja

5. Tawagar Ministoci ta hadar da; Geofferey Onyeama Ministan harkokin kasashen ketare, Mansur Dan-Ali Ministan Tsaro, Kemi Adeosun Ministar Kudi, Abdulrahman Dambazau Ministan harkokin cikin gida da kuma Ministan kasuwanci da masana'antu, Okechukwu Enelamah.

6. Sauran tawagar shugaba Buhari ta hadar da; Babban mai bayar da shawara akan tsaro na kasa, Babagana Monguno, shugaban ma'aikatan tsaro, Abayomi Olanisakin, shugaban hukumar NIA, Ahmed Abubakar da kuma Gwamnan babban bankin Najeriya, Godwin Emefiele.

7. An nada shugaba Buhari sabon shugaban kungiyar kasashen Afirka ta Yamma, inda ya ci gajiyar kujerar shugaban kasar Togo, Faure Gnassingbe.

8. Za a gudanar da taron kungiyar na gaba cikin Birnin Abuja a ranar 21 ga watan Dasumba.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku leƙa shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng