Duniya ina zaki damu: Ta gwammace ta aika shi lahira, data bari ya duba wayarta

Duniya ina zaki damu: Ta gwammace ta aika shi lahira, data bari ya duba wayarta

Wata budurwa mai suna Adaugona Esu yar kimanin shekaru 21 ta fada hannun 'yan sanda a dalilin turo saurayinta data yi taga saman bene mai hawa biyu saboda ya nemi ya duba wayar ta

Duniya ina zaki damu: Ta gwammace ta aika shi lahira, data bari ya duba wayarta
Duniya ina zaki damu: Ta gwammace ta aika shi lahira, data bari ya duba wayarta

Wata budurwa mai suna Adaugona Esu yar kimanin shekaru 21 ta fada hannun 'yan sanda a dalilin turo saurayinta data yi taga saman bene mai hawa biyu saboda ya nemi ya duba wayar ta.

Lamarin ya afkune a ranar 13 ga watan Yuli a Ajangbadi dake jihar Legas.

Saurayin mai suna Wilson Henry ya karya wuya da kashin gadon bayansa, sannan bayan kwana uku ya rasu a asibitin koyarwa dake Ikeja a jihar Legas (LASUTH).

Budurwa dai tana zaune tare da tsohon saurayin ta mai suna Eto a gidan dake Origa Street kafin yabar kasar a watan Yuli 2017.

Daga nan ne ta fara soyayya da Henry wanda ya gama karatun sa na jami'a a bangaren engineering a jami'ar Benin.

DUBA WANNAN: Zamu kawo karshen rashin tsaro a yankin Birnin Gwari da Zamfara - Buratai

A ranar da abun ya faru Henry ya kawowa budurwar tashi ziyara inda ya nemi ya karbi wayar ta daganan suka fara rigima.

Tace "Yazomin a buge inda ya nemi in bashi wayata ya duba ni kuma naki, inata kokarin hanashi wayar sai ya fara duka na ni kuma na fara ihu ina neman agaji.

"Banyi wani ihu sosai ba makotana suka balle kofar, Henry ya gudu cikin daki sannan yayi tsalle ya dira ta taga.

"Bani ce na turashi ba da ace nina turashi dole tagar zata fashe. Ya dira ta taga din ne saboda yana tsoron Roy, bansan yaji ciwo ba saida na fita na ganshi a kwance ya kasa motsi."

Na kaishi asibitin Crown inda aka bashi taimako amma kuma baya iya motsa komai a jikinsa sannan yace bayajin wani ciwo, har lokacin da likita yayi masa allura baiji komai ba.

Daganan ne aka maidashi asibitin koyarwa na jihar Legas (LASUTH) Inda ya rasu bayan kwana Uku da afkuwar lamarin.

Yanzu haka hukumar yan sanda suna tuhumar Esu da hallaka saurayin nata ta hanyar jefoshi ta taga.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel