Babban ‘Dan ganin-kashe nin Saraki Bolaji Abdullahi yace bai bar APC ba tukuna
Mun ji labari cewa Kakakin Jam’iyyar ACP mai mulki watau Bolaji Abdullahi ya musanta cewa ya fice daga Jam’iyyar. Bolaji Abdullahi yace har gobe yana nan a matsayin sa na ‘Dan Jam’iyya har gobe.
Bolaji Abdullahi ya bayyanawa manema labarai a Birnin Tarayya Abuja cewa abin da ake fada na cewa ya sauya sheka ba gaskiya bane sam. An dai fara rade-radin cewa Abdullahi ya koma Jam’iyyar PDP mai adawa a jiya.
Wannan rade-radi ya fara yawo ne bayan da Mai magana da yawun Jam’iyyar ya gaza halartar wani babban taro da manyan APC da aka yi a farkon makon nan. An dai nemi Sakataran yada labaran a taron na APC an rasa.
KU KARANTA: Atiku yayi farin cikin jin cewa Saraki ya bar APC
Abdullahi dai ya bayyana cewa kawo yanzu yana nan da-ram-dam a Jam’iyyar da ke mulkin kasar duk da cewa Mai gidan sa watau Shugaban Majalisar Dattawa Dr. Bukola Saraki ya tsere daga Jam’iyyar jiya ya koma PDP.
Mista Abdullahi ya bayyana cewa ba sa da niyyar barin APC ko kadan inda yace kamar yadda ya shigo ta kofa, haka zai bar Jam’iyyar ta kofa idan ta kama. Tsohon Ministan yace bai halarci taron APC bane saboda yayi tafiya
Mai magana da bakin APC Mista Bolaji Abdullahi ya bayyana cewa ba sa da niyyar barin APC ko kadan inda yace kamar yadda ake fada. Kun san cewa dai PDP tayi murna da dawowar Shugaban Majalisar Dattawa Bukola Saraki.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng