Babban sufetan Yansanda ya daga Dansandan dake Tafsirin Al-Qur’ani zuwa mukamin Kwamishina

Babban sufetan Yansanda ya daga Dansandan dake Tafsirin Al-Qur’ani zuwa mukamin Kwamishina

Babban sufetan Yansandan Najeriya ya amince da nadin Ahmad Abdulrahman a matsayin sabon kwamishinan Yansandan jihar Kaduna, wanda ya canji kwamishina mai barin gado, Austin Iwar kamar yadda Legit.ng ta kalato.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito Kaakkain rundunar Yansandan jihar, Sabo Yakubu ne ya bayyana haka a ranar Alhamis, 9 ga watan Agusta cikin wata sanarwar da ya fitar, inda yace Ahmad ya karbi ragamar iko tun a ranar 6 ga wata.

KU KARANTA: Gwamnatin Buhari ta mayar da yan Najeriya tamkar mazauna gidan Yari - Tambuwal

Babban sufetan Yansanda ya daga Dansandan dake Tafsirin Al-Qur’ani zuwa mukamin Kwamishina

Kwamishina

Shi dai Dansanda Ahmad ya kasance yana gudanar Tafsirin Al’Qur’ani a duk watan Azumin Ramadan a babban Masallaci dake shelkwatar rundunar Yansandan jihar Kaduna, inda yake fassara Al’Qur’ani da ilimi iya gwargwado.

An haifi Ahmad a garin Kirfi na jihar Bauchi, kuma ya shiga aikin Dansanda a shekarar 1990 bayan ya yi karatun digiri a jami'ar Usmanu Danfodiyo dake Sakkwato, sa'annan yayi karatun digiri na biyu a jami'ar jihar Kaduna.

A wani hira da aka taba yi da Ahmad, yace babban dalilin shigarsa aikin Dansanda shine tun bayan wani rikici da aka taba yin a Zangon Kataf a jihar Kaduna, inda yace Sojoji suka kama su ana wannan rikicn, basu sake sub a har sai mariyagi Malam Abubakar Mahmud Gumiya kwace su da kyar.

Ahmad yace bayan Malam ya kwacesu ne sai yake basu shawarar su shiga aikin Soja da Dansanda don su kare mutuncin addininsu, ya jaddada musu cewa da akwai nasu a aikin ba za’a dinga ci musu mutunci ba, “Daga nan na yanke shawarar shiga aikin Dansanda.” Inji shi.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel