Zakarar da Allah ya nufa da cara: Wata yarinya ta tsere daga hannun mayakan Boko Haram

Zakarar da Allah ya nufa da cara: Wata yarinya ta tsere daga hannun mayakan Boko Haram

Ikon Allah sai kallo, zakaran da Allah ya nufa da cara, ko ana mazuru ana shaho sai ya yi, wannan shine kwatankacin lamarin da ya faru a a ranar Lahadi, 29 ga watan Yuli a jihar Borno.

Wata yarinya mai shekaru 15, Zainab Mohammed ta gudo daga sansanin mayakan kungiyar yan ta’adda na Boko Haram bayan shafe tsawon lokaci a hannunsu, inda ta fada hannun Dakarun Sojojin Najeriya, kamar yadda Legit.ng ta ruwaito.

KU KARANTA: Nahiyar Turai ta baiwa El-Rufai tallafin naira biliyan 4.2 don kammala wani muhimmin aiki

Zakarar da Allah ya nufa da cara: Wata yarinya ta tsere daga hannun mayakan Boko Haram

Zainab

Rundunar Sojin kasan Najeriya ta bakin Kaakakinta, Birgediya texas Chukwu ne ya sanar da haka a ranar Lahadin, inda yace: “mayakan runduna ta 28 na rundunar Sojin Najeriya sun ceci wata yar barinya da ta tsere daga sansanin mayakan Boko Haram a kauyen Gulba.”

Sa’annan Kaakaki Texas ya karkare batunsa da cewa: “Zamu mikata ga hukumar da ta dace da zarar mun kammala gudanar da bincike akanta.” Inji shi.

A wani labarin kuma, Birgediya Texas ya bayyana cewa Sojoji sun kawar da wani da hari da mayakan Boko Haram suka kai musu a jihar Borno, inda suka kashe yan ta’adda da dama, sa’annan suka kwato bindiga kirar AK 47 da alburusai da dama.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel