Jerin Matan da su ka fi kowa kudi a fadin Duniya

Jerin Matan da su ka fi kowa kudi a fadin Duniya

Wannan karo mun kawo maku jerin matan da su ka fi kowa arziki a Duniya. Ta farko a jerin ita ce Alice Walton wanda ta gaji dukiya daga Mahaifin ta. Dama kun san cewa Jeff Bezos ya kerewa Bill Gates a sahun maza.

Jerin Matan da su ka fi kowa kudi a fadin Duniya
Alice Walton mai kamfanin nan Walmert da ake ji da shi

1. Alice Walton

A shekarar 2018 Alice Walton ce ta cigaba da rike kanbun ta inda arzikin ta ya karu daga Dala Biliyan 33 zuwa Dala Biliyan 46. Hannun jarin kamfanin Walmart ne ya kara kudi a Duniya a shekarar nan.

2. Francoise Bettencourt Meyers

Francoise Meyers ta ba sama da Dala Biliyan 42 baya kamar yadda Mujallar Forbes ta bayyana wannan shekarar. Asalin Iyayan Francoise Meyers ‘Yan kasuwa ne da su kayi fice wajen harkar kwalliya tun a 1909.

KU KARANTA: Sarakunan Najeriya na ganawa da Shugaban kasa

3. Susanne Klatten

Susanne Klatten ce ta uku a wannan jeri kuma ita ma kamar sauran Takwarorin ta, tayi gadon dukiyar ta ne daga Iyayen ta. Forbes ta rahoto cewa Klatten ta ba akalla Dala Biliyan 25 baya a yanzu da mu ke magana.

Sauran Attajiran da ake ji da su a cikin manyan matan Duniya sun hada da Maria Franca Fissolo, Laurene Powell Jobs, Kirsty Bertarelli da Denise Coates wanda ta ba Dala Biliyan 5.

Kwanaki kun ji cewa Jeff Bezos Mai kamfanin nan na Amazon ya kafa tarihi inda ya zama wanda ya fi kowa mallakar dukiya a tarihin Duniya inda ya tara abin da ya haura Dala Biliyan 100.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel