Dan takarar gwamna a PDP ya yi korafin cigaba da tsare shi ga IG
Dan takarar gwamna a jam'iyyar PDP a jihar Borno da 'yan sanda suka kama, Grema Terab, ya yi korafi ga Sufeta Janar na 'yan sandan Najeriya da kuma hukumar kula da ayyukan 'yan sanda na kasa kan tsare shi da hukumar 'yan sandan jihar Borno tayi.
An dai kama Terab saboda zarginsa da hannu cikin kisan wani mutum da akayi a wata taron 'yan siyasa da ya shirya a gidansa dake Maiduguri kimanin wattani uku da suka gabata.
An kama shi ne a wata taron 'yan siyasa da tsohon shugaban kasa Atiku Abubakar da sauran mambobin PDP na jihar Borno shirya.
KU KARANTA: Fashin Offa: Ministan shari'a Malami ya wanke Saraki
A cewar kwamishinan 'yan sandan jihar Borno, Damian Chukwu, an cafke Terab wajen taron 'yan PDP da Atiku saboda yaki amsa gayyatar da hukumar 'yan sandan tayi masa don ya amsa tambayoyi game da kissar gillar da akayi a gidansa.
A wasikar da lauyoyin Terab, Abdulmalik Avoswahi & Co suka shigar a Abuja a ranar 19 ga watan yulin shekarar 2018, lauyoyin sun janyo hankalin Sufeta Janar na 'yan sandan cewa kotu tayi hani da 'yan sandan su kama Terab, saboda haka kamun da a kayi masa ya sabawa doka.
Lauyoyin Terab sun aike da irin wasikar ga fadar shugaban kasa da hukumar kiyaye hakkin bil-adama da Amnesty International da jakadar kasar Amurka dake Najeriya da wasu wurare inda suke bukatar a saki dan takarar da 'yan sanda ke tsare dashi.
A wata labarin kuma, Legit.ng ta kawo muku rahoton yadda hukumar 'yan sanda reshen jihar Legas ta gurfanar da Ciyaman din jam'iyyar PDP na jihar Moshood Salvador a gaban kotu bisa tuhumarsa da kashe ciyaman din jam'iyyar na karamar hukuma Apapa, Adeniyi Aborishade.
An dai kashe Aborishade ne sakamakon fada da ta kaure tsakanin magoya bayansa da na Salvador a wata taron jam'iyyar da aka gudanar a kauyen Igbosuku dake karamar hukumar Eti-Osa na jihar.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng