Aliyu Gebi ya janye takarar sa na Sanatan Bauchi ta Kudu sai zuwa zaben 2019

Aliyu Gebi ya janye takarar sa na Sanatan Bauchi ta Kudu sai zuwa zaben 2019

Yayin da ake shirin shiga takarar kujerar Sanatan Yankin Kudancin Jihar Bauchi mun samu labari jiya cewa daya daga cikin ‘Yan takarar ya janye inda ya koka da irin makudan kudin da ake bukata wajen lashe zaben fitar da gwani.

Aliyu Gebi ya janye takarar sa na Sanatan Bauchi ta Kudu sai zuwa zaben 2019

Wani daga cikin masu neman kujerar Ali Wakili ya janye takara

Honarabul Aliyu Ibrahim Gebi yana cikin masu burin maye gurbin Sanata Ali Wakili wanda ya rasu kwanaki. Hpnarabul Gebi yanzu ya hakura saboda yadda aka tsawwala kashe mahaukatan kudi kafin mutum ya samu tikitin takara.

Tsohon ‘Dan Majalisar Tarayyar ya nuna cewa ba zai yi wannan takara da za ayi ba na kwanan nan amma ya tabbatar da cewa da su za a buga a zaben 2019. Aliyu Gebi ya nuna takaicin san a cewa ‘Dan takarar da ya fi kudi ne zai yi nasara.

KU KARANTA: Shugabannin tsaro na tashi da Biliyoyin kudi duk shekara

Aliyu Gebi wanda ya wakilci Jihar Bauchi Majalisar Tarayya shekaru 7 da su ka wuce a karkashin Jam’iyyar CPC ya nemi a kawo gyara a yadda ake gudanar da siyasar kasar. Hon. Gebi ya kuma nemi a rika bari Talakawan Gari sun yi zaben fitar da gwani.

A baya kun taba ji cewa ‘Yan takara kusan 30 ke neman takarar kujerar Sanatan Bauchi. Tsohon Gwamnan Jihar Bauchi a PDP Isa Yuguda zai fito takarar Sanatan na Bauchi a karkashin Jam’iyyar GNPP. Irin su Bala Muhammad ma za su nemi kujerar.

Dazu kun ji labari cewa a siyasar Kano an fara kokarin dawo da Ibrahim Shekarau Jam’iyyar APC kafin 2019. Hakan zai rusa tsohon Gwamna Rabiu Kwankwaso da ya sauya sheka zuwa PDP kwanan nan.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel