Kowa ya bar gida: Guda cikin Sanatoci 15 da suka fice daga APC ya yi mi’ara koma baya

Kowa ya bar gida: Guda cikin Sanatoci 15 da suka fice daga APC ya yi mi’ara koma baya

Sanata Lanre Tejuso, guda cikin Sanatocin nan su goma sha biyar dya fice daga jam’iyyar APC zuwa jam’iyyar PDOP kamar yadda shugaban majalisar dattawa Sanata Bukola Saraki ya bayyana, ya yi mi’ara koma baya, ya koma jam’iyyarsa ta APC.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Tejuso, wanda shine dan majalisa mai wakiltar al’ummar Ogun ta tsakiya ya tabbatar da dawowarsa cikin jam’iyyar APC ne a daren Laraba, 25 ga watan Yuli yayin wata ganawa da Sanatocin jam’iyyar APC suka yi da shugaban kasa Muhammadu Buhari a fadar gwamnati.

KU KARANTA: Ruwa ba sa’an Kwando ba: Daliban Kaduna sun lallasa na kasar Amurka a gasar Duniya

Kowa ya bar gida: Guda cikin Sanatoci 15 da suk fice daga APC ya yi mi’ara koma baya
Sanata Lanre da Buhari

Dayake jawabinsa a yayin taron, Sanata Tejuosu ya bayyana ma shugaba Buhari cewa: “Ya maigirma shugaban kasa, ni danka ne, kuma na dawo gida.” Sa’annan ya kara da cewa ya halarci wannan taro ne don ya jaddada zamansa a cikin jam’iyyar APC.

Bugu da kari, an hangi Sanata mai wakiltar Oyo ta kudu, Sanata Adesoji Akanbi a yayin wannan taro, wanda shima Sanata Saraki ya bayyana sunansa a cikin Sanatocin da suka yi watsi da APC, inda yace tuggu ce kawai ta yan siyasa ya sanya Saraki ambatar sunansa, amma yana cikin APC tsundum.

Shima fitaccen dan gwagwarmaya, Sanata Shehu Sani ya halarci wannan taro, duk dayake an sha jin amonsa yana sukar jam’iyyar APC, sauran wadanda suka halarci wannan zama sun hada da Adamu Aleiro, Bala Ibn Na-Allah, Aliyu Wamako, Ibrahim Gobir, Kabiru Marafa, Abu Ibrahim, Kabiru Gaya, Barau Jibrin, Abdullahi Gumel, Ahmed Lawan, Ali Ndume, Abubakar Kyari, Baba Kaka Garbai, Aliyu Abdullahi, David Umaru da Abdullahi Adamu.

Kowa ya bar gida: Guda cikin Sanatoci 15 da suk fice daga APC ya yi mi’ara koma baya
Adesoji da Lanre da aka ce sun fita

Sauran sune George Akume, Francis Alimekhina, Andrew Uchendu, Magnus Abe, Ovie Omo-Agege, John Enoh, Nelson Effiong, Andy Uba, Sunny Ugboji, Hope Uzodinma, Ben Uwajimogu, Yusuf Abubakar, Oluremi Tinubu, Gbenga Ashafa, Solomon Adeola, Tayo Alasoadura, Ajayi Boroffice , Yele Omogunwa, Fatima Rasaki, Olanrewaju Tejuoso da Yahaya Abdullahi.

Shugaba Buhari ya kira wannan taro ne bayan ficewar Sanata Rabiu Musa Kwankwaso tare da wasu Sanatoci goma sha biyu daga APC zuwa jam’iyyar PDP, sai dai ba a hangi keyar Saraki ba, wanda ake ganin shima yana gab da jefar da APC ya rungumi PDP.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Tags:
APC