Majlisar dinkin duniya ta aiko likitoci Najeriya don aiki kyauta ga masu yoyon fitsari
- UNFPA ta kawo wasu manyan likitoci guda Uku zuwa jahar Borno dan magance cutar yoyon fitsari ga mata
- Likitocin zasu duba mata 150 dake fama da yoyon fitsari
- Aikin nasu zai kai tsayin sati biyu
UNFPA ta samu nasarar gayyato Likitoci guda uku daga kasar Faransa zuwa jahar Borno don duba mata masu fama da lalurar yoyon fitsari.
Likitocin sun hada da Prof Alain Le Duc, Dr Claude Demurger da Dr Ludovic Falandry wanda dukkanin su sun gama aiki a kasar ta Faransa.
Zasu duba mata 150 dake dauke da cutar ta yoyon fitsari sannan su horar da likitocin jahar ta Borno akan harkar.
DUBA WANNAN: Kudin da aka kashe don dawo da jirgin Najeriya
Mata kusan 150,00 ke fama da wannan ciwon a fadin kasar nan wanda da suna samun kulawa da hakan Yazo karshe.
Basu da wani sauran jindadi a rayuwar su, abunda kawai zai dawo musu da wannan shine aikin da za'ayi musu.
Kulawa da mata masu juna biyu wadanda basukai haihuwa ba ka iya dakile samuwar ciwon a garesu.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng