Tsohon Gwamna Kwankwaso ya raba kan ‘Yan Majalisar Kano
A jiya ne wasu manyan ‘Yan Majalisar Tarayya su ka tattara su ka sauya sheka daga Jam’iyyar APC mai mulki su ka koma PDP. Daga cikin wadanda su ka bar APC akwai tsohon Gwamnan Jihar Kano Sanata Rabiu Musa Kwankwaso.
Sanatoci fiye da 10 ne su ka bar APC, daga ciki akwai Sanatocin Bauchi, Jigawa, Adamawa da wasu Sanatoci daga Jihar Kwara. Bayan nan kuma akwai ‘Yan Majalisar Wakilan Tarayya da su ka bi sahu su ka arce zuwa Jam’iyyar PDP.
KU KARANTA: Babban abin da ya hana Shugabannin Majalisar Najeriya tserewa daga APC
Daga cikin ‘Yan Majalisar Wakilan da su ka bar APC su ka koma PDP akwai wasu mutum 10 daga Jihar. ‘Yan Majalisar Tarayyan sun bi tsohon Gwamnan Jihar Kano kuma Shugaban tafiyar Kwankwasiyya watau Sanata Rabiu Kwankwaso.
Ga dai jerin ‘Yan Majalisar na Kano da su ka bi tsohon Gwamna Rabiu Musa Kwankwaso kamar yadda Jaridar The Cable ta kawo su:
1 Garba Muhammed Kano PDP
2 Ado Tsamiya Musa Kano PDP
3 Shehu Usman Kano PDP
4 Garuba Bichi Kano PDP
5 Musa Ado Kano PDP
6 Garuba Umar Kano PDP
7 Dambaram Nuhu Kano PDP
8 Nasir Sule Kano PDP
9 Aliyu Madaki Kano PDP
10 Sani Rano Kano PDP
Akwai dai wasu ‘Yan Majalisar Tarayya 14 daga Kano wanda har yanzu su na tare da Jam’iyyar APC mai mulkin Jihar. Daga cikin manyan ‘Yan Majalisun akwai irin su Alhassan Ado Dgouwa, Abdulmumin Jibrin, Nasir Babale, Bashir Babale da sauran su.
Kun san cewa a 2014 ne Kwankwaso ya bar PDP lokacin yana Gwamna inda shi kuma tsohon Gwamna Ibrahim Shekarau ya bar APC ya koma PDP. Yanzu dai duk sun samu kan su a PDP bayan Kwankwaso ya samu matsala da Gwamna Abdullahi Ganduje.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng