Ba a rabu da bukar ba: Cikas din da Kwankwaso zai gamu da su bayan ya bar APC

Ba a rabu da bukar ba: Cikas din da Kwankwaso zai gamu da su bayan ya bar APC

Mun kawo maku wasu cikas da ake tunani cewa tsohon Gwamnan Kano Rabi’u Musa Kwankwaso zai gamu da su bayan ficewar sa daga Jam’iyyar APC inda ya koma PDP inda ya fito.

Ba a rabu da bukar ba: Cikas din da Kwankwaso zai gamu da su bayan ya bar APC
Tsohon Gwamna Kwankwaso ya samu sabani da Mataimakin sa a da

A 2014 ne Rabiu Kwankwaso ya bar PDP lokacin yana Gwamnan Jihar Kano inda shi kuma tsohon Gwamna Ibrahim Shekarau ya bar Jam’iyyar adawa a lokacin na APC ya koma PDP. Yanzu dai duk sun samu kan su a PDP.

1. Muhammadu Buhari

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari na iya takawa Rabiu Kwankwaso burki idan su ka hadu a zaben 2019. A 2014, Kwankwaso ya sha kashi a hannun Buhari a zaben fitar da gwani na APC. Da wahala Kwankwaso ya iya buge Buhari.

KU KARANTA: Wasu Matasan Arewa sun yi kaca-kaca da Gwamnatin Buhari

2. Atiku Abubakar

Tun a bara ne tsohon Mataimakin Shugaban Kasa Atiku Abubakar ya fice daga APC ya dawo PDP. Da alamu dai sai Kwankwaso yayi da gaske zai iya samun tikiti daga hannun Atiku Abubakar da sauran ‘Yan takarar Jam’iyyar PDP.

3. Ibrahim Shekarau

Yanzu dai tsohon Gwamna Ibrahim Shekarau kusan shi ne Shugaban Jam’iyyar PDP a Kano. Shekarau da Kwankwaso ba a shiri a da kuma duk watakila su nemi kujerar Shugaban kasa. Yanzu dai dole Kwankwaso ya koma kasan Shekarau a Kano.

A jiya da dare kun samu labari cewa tsohon Gwamnan Jihar Kano Rabiu Musa Kwankwaso ya gana da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari a cikin fadar Shugaban kasar na Aso Villa amma sai ga shi yau ya fice daga APC.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng