Gwamna Fayose ya tofawa ‘Yan Majalisan da su ka tsere daga APC albarka
- Gwamna Fayose ya yabawa wadanda su ka fice daga APC
- Wasu manyan ‘Yan APC sun tsere daga Jam’iyyar a yau
- Jam’iyyar APC ta rasa ‘Yan Majalisan ta zuwa PDP dazu
Mun samu labari cewa Gwaman Jihar Ekiti mai shirin barin kujera watau Adodele Fayose ya fito daga buyan da yayi inda yayi magana kan ficewar wasu manyan ‘Yan Majalisa daga Jam’iyyar APC ta shafin sa na Tuwita dazu nan.
Dazu ne wasu manyan Sanatoci fiye da 10 su ka tattara su ka bar Jam’iyyar APC. Daga cikin wadannan Sanatoci akwai tsohon Gwamnan Jihar Kano Sanata Rabiu Musa Kwankwaso da Sanatocin Jihar Kaduna da Bauchi.
KU KARANTA: An bankado yadda ake cuwa-cuwa wajen harkar kwallon Najeriya
Gwamnan Ekiti Ayo Fayose yayi farin ciki da wannan labari inda yace an kusa kawo karshen mulkin danniya a Kasar. Gwamnan yana nuni ne da Gwamnatin APC ta Shugaban Kasa Buhari da yake zargi da kama-karya a Kasar.
Ayo Fayose ya sa wa ‘Yan Majalisun da su ka koma PDP albarka inda ya jinjinawa Shugaban Majalisar Dattawan Kasar. Gwamnan wanda Jam’iyyar sa ta kasa a zaben Gwamna kwanan yace yana yi sababbin ‘Yan PDP fatan sa’a.
A Majalisar Wakilai ma akwai wadanda ake tunani sun fice daga APC. ‘Yan Majalisun sun hada da: Emmanuel Orker-Jev, Sani Rano Barry Mpigi, Ali Madaki, Hassan Saleh, Danburam Nuhu, Mark Gbilah, da kuma Hon. Razak Atunwa
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng