Duka biyu: Majalisar Dattawa ta yi watsi da wata bukatar da Buhari ya nema a gareta

Duka biyu: Majalisar Dattawa ta yi watsi da wata bukatar da Buhari ya nema a gareta

A ranar Talata 24 ga watan Yuli ne kafatanin Sanatoci suka bayyana rashin amincwarsu da wani mutumi dan jihar Legas da wata muhimmiyar bukata da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya aiko musu, wanda hakan ya sanya dole majalisar ta yi watsi da wannan bukata.

Legit.ng ta ruwaito shugaba Buhari ya aika ma majalisar da sunan wani jigon jam’iyyar APC a jihar Legas, Muiz Banire don su tantance shi kafin ya nada shi mukamin shugaba hukumar kwato kadarorin gwamnati, AMCON.

KU KARANTA: Zamanin sauyin sheka: Yan majalisar APC guda 37 sun sheke zuwa PDP

Sai dai da alama Buhari bai bibiyi Sanatocin ba, wanda hakan ya sanya dukkanin Sanatoci guda uku da suka fito daga jihar Legas suka nuna rashin amincewarsu da wannan mutumi, sa’annan suka mika ma majalisar takardar korafi a game da shi.

Duka biyu: Majalisar Dattawa ta yi watsi da wata bukatar da Buhari ya nema a gareta

Muiz Banire

Sanatan Solomon Adeola ne ya fara yin bore ga wannan bukata ta shugaban kasa, inda yace: “Akwai korafe korafe daga mazabata game da nadin Muiz Banire a matsayin shugaban AMCON, haka zalika duka Sanatocin jihar Legas guda uku bamu amince da shi ba.”

A jawabinsa, shugaban majalisar dattawa, Sanata Bukola Saraki ya umarci Sanatocin da su aika korafe korafensu zuwa kwamitin ladabtarwa ta majalisar dattawa don dubawa.

A ranar 18 ga watan Yuli ne majalisar ta amshi bukatar da Buhari ya aiko mata na tantance Banire, inda daga bisani kwamitin majalisar dake kula da harkokin kudi ta tantance shi, amma ga shi yanzu yana fama da kalubale.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel