Jan kunne: Idan Buhari na daukar raini, toh ni bani daukar raini – Inji shugaban APC Oshiomole

Jan kunne: Idan Buhari na daukar raini, toh ni bani daukar raini – Inji shugaban APC Oshiomole

Farawa da iyawa, sabon Shugaban jam’iyyar APC, Adams Oshiomole ya gargadi ministocin shugaban kasa Muhammadu Buhari game da yadda suke tafiyar da ma’aikatunsu, inda yayi barazanar fatattakarsu daga jam’iyyar.

Legit.ng ta ruwaito Oshimole yayi wannan jan kunne a ranar Litinin, 23 ga watan Yuli a fadar shugaban kasa, inda yace ministocin Buhari na amfani da damar da Buhari ya basu na cikakken iko suna yadda suka gadama a ma’aikatunsu, don yace zai nemi Buhari ya dauki mataki akan ire iren ministocin nan.

KU KARANTA: Wani matashi ya zartar da hukuncin Zina akan wasu abokansa guda 2

Ya kara da cewa idan shugaba Buhari zai lamunci rainin da Ministocin suke masa, shi kam ba zai lamunta, don kuwa jam’iyyar APC a karkashin jagorancinsa ba zata zura ido tana kallon ministoci suna cin mutuncin ofishinsu ba, tare da kin yi ma shugaba Buhari biyayya, ta hanyar kin zartar da umarninsa.

Jan kunne: Idan Buhari na daukar raini, toh ni bani daukar raini – Inji shugaban APC Oshiomole

Buhari da Oshiomole

“Ya zama dole mu tabbatar da da’a da biyayya a cikin jam’iyyarmu, ba zai yiwu don kana minister ka dinga shirme ba, babu wani da yafi karfin jam’iyya, idan Buhari yana jure rashin kunyarsu, ni kam b azan lamunci a ci mutuncin jam’iyya ba

“Idan kuma muka sallami minista daga jam’iyyarmu, zan fada ma Buhari ya sallame shi, don kuwa ba zamu cigaba da zama tare da duk wani mutumi mara mutunci da baya mutunta shi tare da jam’iyya ba.” Inji shi.

Oshimole yayi wannan korafi ne bisa rashin kaddamar da kwamitociin gudanarwar hukumomi da cibiyoyin gwamnati da ministoci suka ki yi, alhalin shugaba Buhari ya nada mutanen da zasu cike guraben hukumomin tun lokaci mai tsawo daya gabata.

Daga karshe ya bukaci dukkan ministocin da wannan batu ya shafa, da su tabbata sun kaddamar da wadannan kwamitoci, domin a cewarsa da haka suke fakewa suna bayar da kwangiloli ba tare da sa idon kwamitocin ba, idan ba haka ba zasu sa wando daya dasu.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel