Allah ya takaita: Ministan Buhari ya tsallake rijiya da baya yayinda hatsarin mota ya ritsa da shi

Allah ya takaita: Ministan Buhari ya tsallake rijiya da baya yayinda hatsarin mota ya ritsa da shi

Mutum daya ya rasu, wasu 20 kuma sun sami munanan raunuka a wata hatsarin mota da ta faru da motocin tawagar ministan matasa da wasanni, Solomon Dalung a jihar Gombe.

Cikin wandanda suka jikkata har da shugaban rikon kwarya na majalisar matasan Najeriya na NYCN, Chinedu Mayor.

Wani jami'in tsaro a jihar ta Gombe, Sunday Jika, wanda ke cikin tawagar ministan wasanni da matasan ne ya tabbatar da afkuwar hatsarin a wata hira da ya yi da manema labarai a Gombe.

Allah ya takaita: Ministan Buhari ya tsallake rijiya da baya yayinda hatsarin mota ya ritsa da shi

Allah ya takaita: Ministan Buhari ya tsallake rijiya da baya yayinda hatsarin mota ya ritsa da shi

Jika yace, "Mun tarbo minisatan ne daga filin tashin jiragen sama muna hanyar mu ta komawa cikin gari sai wata mota kirar Peugeot 406 ta shigo cikin tawagar ministan ta gogi motar da ke gabanmu.

"Peugeot din ta kama da wuta nan take, munyi kokari mun ceto mutane uku daga cikin motar amma direban ya kone tare da motar.

DUBA WANNAN: Cikin hoto: An yi mummunan hatsarin mota tsakanin motar Dangote da ta fasinjoji, da dama sun mutu

"A dayar bas din dake tawagar ministan, mun ciro wasu mutane. Dukkan wadanda suka sami rauni suna asibitin kwararu na Gombe da Asibitin koyarwa na tarayya FTH suna karban magani."

Wani jami'in kamfanin dillancin labarai na kasa NAN, ya tafi asbitocin biyu kuma ya ga likitoci na kulawa da wadanda hatsarin ya ritsa dasu.

Mataimakiyar shugaban asibiti koyarwa na tarayya, Dr. Zainab Kaltungo, taki cewa komai lokacin da aka tuntube ta.

Kazalika, Godwin Omiko, kwamandan hukumar kiyaye haddura na kasa FRSC reshen jihar Gombe, yace bai da masaniya game da afkuwar hatsarin a halin yanzu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel