'Yan bindiga sun harbe babban limami a jihar Filato
A daren ranar Laraba ne wasu 'yan bindiga da ba'a san ko su wanene ba suka harbe babban limamin garin Bachi dake karamar hukumar Riyom na jihar Filato.
Marigayi Alhaji Abdullahi Abubakar ba boyeye bane a jihar musamman yadda ya yi suna wajen kira a zauna lafiya da kuma hallartan taron sulhu tsakanin Fulani da 'yan kabilar Birom da masu sassan jihar.
Shugaban kungiyar Miyetti Allah na jihar, Alhaji Ibrahim Mato, ya shaidawa Daily Trust cewa marigayi Abubakar mutum ne mai son zaman lafiya da hadin kan al'umma hakan yasa kowa ke mutunta shi.
DUBA WANNAN: Ku rage yawan haihuwa domin 'ya'yanku su samu ilimi - Ganduje
Ya ce 'yan bindigan sun kutsa kai ne cikin gidan babban malamin misalin karfe 10 na dare kuma suka harbe shi har lahira.
Jami'an yadda labarai na Operation Safe Haven, Manjo Adam Umar, yace shugaban kungiyar Miyetti Allah na Riyom na kawo masa rahoton rasuwar.
Ya kara da cewa jami'an hukumar sojin sun fara gudanar da bincike tare da 'yan sanda don ganin an gano wadanda suka aikata wannan mummunan aikin.
A wani rahoton, Legit.ng ta kawo muku rasuwar tsohon Sufeta Janar na Yan sandan Najeriya, Alhaji Ibrahim Coomassie, marigayin ya rasu ne a jihar sa ta Katsina bayan ya yi fama da gajeruwar rashin lafiya.
Anyi jana'izar Coomassie a ranar Juma'a 20 ga watan Yulin shekarar 2018 a jihar Katsina.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng