Farawa da iyawa: Wasu 'yan takarar PDP sun janye bisa zargin rashin adalci

Farawa da iyawa: Wasu 'yan takarar PDP sun janye bisa zargin rashin adalci

Wasu daga cikin 'yan takaran gwamna na jam'iyyar PDP a jihar Osun sun janye daga takarar gabanin fara zaben fidda gwani.

Wasu daga cikin wadanda suka sanar da janyewarsu daga takarar zaben sun hada da Farfesa Adeolu Durotoye; tsohon ministan cigaban matasa, Mr Olasunkanmi Akinlabi da kuma Felix Ogunwale.

Sauran kuma sune, Cif Lere Oyewunm; tsohon kakakin majalisar jihar Osun da kuma Mr Adejare Bello da Ayoade Adewopo.

Farawa da iyawa: Wasu 'yan takarar PDP sun janye bisa zargin rashin adalci

Farawa da iyawa: Wasu 'yan takarar PDP sun janye bisa zargin rashin adalci

KU KARANTA: Hajjin Bana: Yau za a fara jigilar maniyyatan Najeriya, duba hotuna

Yanzu 'yan takarar da zasu gwabza a zaben sune Senata Ademola Adeleke; tsohon sataren gwamnatin jihar Osun, Alhaji Fatai Akinbade; Shugaban Mutual Assurance, Dr Akin Ogunbiyi da Mr Nathaniel Oke (SAN).

Ciyaman din gudanar da zaben fidda gwani na jihar, Seriake Dickson, wanda tsohon gwamna ne a jihar Bayelsa ya yi alkawarin cewa za'a gudanar da zaben cikin aminci ba tare da wata kunbiya-kunbiya ba.

Yace deleget zasu kada kuri'a kuma duk wanda yafi samun kuri'u zai kasance dan takarar jam'iyyar ta PDP a zaben da za'a gudanar a ranar 22 ga watan Satumba, ya nanata cewa wanda mutane suka zaba shine za'a bawa tikitin.

Delegets daga matakin tarayya da na jihohi sun fara kada kuri'unsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel