‘Yan kasuwar Kano za su marawa Salihu Takai baya a zaben Gwamna

‘Yan kasuwar Kano za su marawa Salihu Takai baya a zaben Gwamna

- ‘Dan takarar Gwamnan Kano a Jam’iyyar PDP ya samu gudumuwa

- ‘Yan kasuwar Jihar sun ce su na tare da Salihu Sagir Takai a 2019

- Ana dai sa rai ‘Dan takarar ya gwabza da Ganduje a zabe mai zuwa

‘Yan kasuwar Kano za su marawa Salihu Takai baya a zaben Gwamna

‘Yan kasuwa sun yi wa Takai mubaya’a a Jihar Kano

Jiya ne mu ka samu labari daga kujerar Gwamna Abdullahi Ganduje ta girgiza bayan da ‘Yan kasuwar Jihar Kano su ka nuna cewa za su ba wanda ke shirin tsayawa takara a PDP goyon baya. Salihu Takai yana yawon neman goyon bayan Jama'a.

A jiya ne jirgin yakin neman zaben Salihu Sagir Takai ya isa wajen Kungiyoyin Malaman addinin Musulunci a karkashin Sheikh Kakisu Abubakar Ramadan da kuma ‘Yan kasuwan Jihar a karkashin tafiyar Alhaji Abdullahi Mai Alewa.

KU KARANTA: Shugaban kasa Buhari ya riki Saraki ka da ya bar APC

Bayan nan kuma Mai shirin neman Gwamnan ya gana Alhaji Sani Abdussalam wanda ke wakiltar masu magani a Jihar. Mai shirin neman zama Gwamnan ya yaba da kokarin da Mutanen ke yi masa wajen ganin ya samu nasara a zaben 2019.

Daga cikin sauran wadanda su ka halarci wannan taro akwai irin su Tsohon Shugaban kasuwar Singa da Alhaji Abdulazeez Dalha Musa da Abdullahi Mai Alewa da Mansur Soja. Yanzu dai PDP za tayi zaben fitar da gwani na Gwamna a Satumba.

Daga cikin masu harin kujerar Gwamna a karkashin PDP bayan Alhaji Salihu Sagir Takai akwai irin su Umar Musa Mustapha, Bello Sani Gwarzo, Alhaji Garba Yusuf Alhaji Jafar Sani Bello, Alhaji Sadiq Aminu Wali da Alhaji Ahmed S. Aruwa

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel