Kisan Danboko: Sojoji sun halaka wani kasurgumin dan ta’adda a jihar Zamfara

Kisan Danboko: Sojoji sun halaka wani kasurgumin dan ta’adda a jihar Zamfara

Dakarun rundunar Sojin kasa ta Najeriya sun samu nasarar kashe wani gagararren dan bindiga da ya addabi al’ummar garin Yanwaren Daji dake cikin karamar hukumar Tsafe na jihar Zamfara a ranar Alhamis, 19 ga watan Yuli.

Wani ma’abocin kafar sadarwar zamani na Facebook, Aliyu Ahmad ne ya bayyana haka a shafinsa inda yace Sojojin sun kashe wannan Dan bindiga ne mai suna Bello Danboko bayan wata musayar wuta da suka yi da shi a lokacin da ya kai musu harin kwantan bauna.

KU KARANTA: Yan Majalisu zasu binciki Buhari kan zargin nuna son kai a nade naden mukamai

Majiyar Legit.ng ya ruwaito a ranar Alhamis ne Sojoji suka kama wani daga cikin yaran Danboko mai suna Shadari, suna kan hanyar komawa sansaninsu ne sai kawai Danboko ya bude musu wuta daga wata gona da yake labe a ciki.

Kisan Daboko: Sojoji sun halaka wani kasurgumin dan ta’adda a jihar Zamfara
Bello Danboko

Anan fa aka fara musayar wuta a tsakaninsu, inda Sojojin suka yi masa luguden wuta har sai da suka ji shiru daga gonar, inda suka yi zaton dan bindigar ya tsere ne, suka yi gaba, har sai da wani yaro da yazo yin ciyawa ya tsince shi kwance cikin jini, kuma ya ruga cikin gari ya fada ma jam’a.

Samun bayanin yaron keda wuya, sai jama’an garin suka kira Sojoji suka tsegumta musu Danboko ne dan bindigan da suka yi musayar wuta da shi, inda suka garzaya zuwa gonar, suka dauko shi zuwa cikin garin, sa’annan suka bude masa wuta tare da Yaron nasa bayan sun yi musu tambayoyi, kuma sun basu amsa.

Zuwa yanzu dai al’ummar garin Tsafe da kewaye na cikin farin ciki sakamakon kisan wannan dan ta’adda, wanda suka bayyana cewar shine ke gudanar da duk wani kashe kashe da ake yi a yankin Yanwaren Daji.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel